Abdullahi Sule: Zanga-Zanga Ba Za Ta Sauya Nasara ta Ba a Kotun Koli
- Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya magantu kan zanga-zangar da ke gudana a jihar bayan nasarar da ya samu a Kotun Koli
- Sule ya shawarci masu zanga-zangar da su yi koyi da halin dattako irin na yan APC wadanda suka ki yin zanga-zanga a lokacin da ya sha kaye a kotun zabe
- Yayin da yake bayyana cewa zanga-zanga ba za ta sauya nasarar da ya samu ba, ya yi kira ga yan adawa da su zo su hada hannu don ci gaban jiharsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya magantu bayan tabbatar da nasararsa da Kotun Kolin kasar ta yi.
Sule ya ce yan jihar su sani cewa, duk irin zanga-zangar da zasu yi ba za ta sauya komai daga hukuncin da Kotun Kolin ta yanke ba, cewa gwanda su rungumi zaman lafiya domin shi ne mafita gare su.
A yau Juma’a, 19 ga watan Janairu, ne kotun kolin ta tabbatar da nasarar Abdullahi Sule na jamiyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar Nasarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun bayan sanar da hukuncin kotun ne al’amura suka fara sauyawa daga yadda suke a baya kafin hukuncin.
Bayan hukuncin ne dai dandazon matasa suka fara tare hanya tare da cinnawa tayoyi wuta domin adawa da hukuncin kotun kolin, rahoton TheCable.
Yadda Lamarin ya faro
Kotun zabe dai a baya ta kwace nasarar Abdullahi Sule tare da tabbatar da David Ombugadu na jamiyyar PDP a matsayin halastaccen gwamnan jihar.
Sai dai kuma, Sule ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara, inda ita kuma ta dawo masa da kujerarsa.
Kan haka ne Ombugadu ya daukaka kara zuwa Kotun Koli domin ganin an tabbatar da shi a matsayin gwanan.
Da yake magana da manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawa da Shugaban kasa Bola Tinubu, Sule ya ce yayin da mutane da dama ba za su amshi hukuncin Kotun Kolin ba, zanga-zanga ba za ta sauya ta ba.
Jaridar Daily Trust ta nakalto gwamnan na cewa:
"A duk jihar da Kotun Koli ta zartar da hukunci, a duk daya daga cikin jihohin nan, za ka ga wasu mutane suna maurna sannan wasu mutane basa murna."
Legit Hausa ta tattauna da wani dan APC mai suna Malam Yusuf don jin ta bakinsa kan nasarar da jam'iyyarsu ta samu a jihar Nasarawa da kuma zanga-zangar da masu adawa ke yi.
Malam Yusuf ya ce:
"APC ce ke da jihar Nasarawa kawai dai an yi kokarin kawo rudani ne. Kuma dama gaskiyar mutum bata karewa sai dai ace karyarsa ta kare kuma ga shi mun gani a Kotun Koli.
"Yanzu dai kiran da zan yi ga masu zanga-zanga wannan ba shi bane mafita domin dai aikin gama ya gama, Gwamna Sule ya tabbata kan kujerarsa a matsayin halastaccen gwamna.
"Kawai su ajiye makaman yakinsu su zo a gina jihar tare da su. Idan ma sun ki za a yi babu su kuma hakan ba zai sauya zani ba. Allah ya zaunar da mu lafiya yasa hakan ne mafi alkhairi ga kowa."
Kotun Koli: Zanga-zanga ta barke a Nasarawa
A baya mun ji cewa zanga-zanga ta ɓarke a Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa biyo bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan zaben gwamna.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.
An toshe hanyar Lafia zuwa Jos gaba daya yayin da masu zanga-zangar suka kunna wuta don hana matafiya da sauran masu amfani da hanyar wucewa.
Asali: Legit.ng