"Mene Ka Ke Girkawa?" Fitaccen Na Hannun Daman Atiku Ya Ziyarci Buhari a Daura, Hotuna Sun Fito
- Jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), reshen jihar Ogun, Segun Showunmi, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
- A wasu hotuna da suka yadu da shi kansa jigon na PDP ya wallafa, an gano cewa ya kai wa tsohon shugaban kasar ziyarar ban girma ne a gidansa da ke Daura, Jihar Katsina
- Sai dai, ziyarar na sa bai yi wa wasu magoya bayan jam'iyyar PDP dadi ba, wadanda suka rika ragargazarsa da cewa yana shirin sauya sheka ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Daura, Katsina - Segun Showunmi, jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ogun kuma na hannun daman tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya kai ziyarar ban girma ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura, jihar Katsina.
Tsohon mai neman takarar gwamnan a jihar Ogun ya bayyana hakan a shafinsa ta manhajar X a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu.
Kamar yadda Legit Hausa ta gani, Showunmi ya rubuta:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na yini da Baba Mai Gaskiya Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari (GCFR) a gidansa da ke Daura."
Ba a san takamammen abin da suka tattauna ba, amma dai wallafar da ya yi ta tabbatar da cewa sun tattaunawa batutuwa ne da suka shafi gina kasa da inda Najeriya ta dosa ya kuma bayyana tsohon shugaban kasar a matsayin 'Wali na Najeriya' shi kuma 'Sarki Gaskiya.'
Ya rubuta:
"Na masa tambayoyi hudu masu muhimmanci kuma ina alfahari da jajircewarsa da rashin cire rai ga kasarmu. Wannan mutumi shine Wali na Najeriya. Ni kuma nine Sarki Gaskiya."
Masu amfani da intanet sunyi martani
Sai dai, yan Najeriya sun tafi sashin sharhi na jigon na PDP don bayyana abin da ke zukatansu kan ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban kasar.
Wasu sun kwatanta shi da Daniel Bwala, wani na hannun daman Atiku wanda a baya-bayan nan ya ziyarci Shugaba Tinubu a Villa.
Bwala, bayan ganawarsa da Tinubu, ya bayyana cewa zai yi godiya idan Shugaban Kasa zai nada shi mukami.
Ga wasu daga cikin abubuwan da mutane suka ce a intanet
@tolaogunnubi ya rubuta:
"Mene ka ke girkawa?"
Suleiman Ibrahim Abubakar ya rubuta:
"@SegunShowunmi, tabbas ba ka shirya zama dan jam'iyyar hamayya ba. Ba mamaki mutane irin Bwala za su iya fitowa su lashe amansu.
"Buhari mai gaskiya? Wannan shine mutumin da ya jagoranci Najeriya zama babban birnin talauci. Wannan shine mutumin da ya yi aiki da AGF wanda ya sace biliyoyi. Idan kwakwalwarka ba ta da lafiya toh kana fama da ciwon 'mugu illumination deficiency syndrome."
Comr. Abdulazeez Adamu (CAA) ya rubuta:
"Ya ce Mai gaskiya. Ba ni da matsala da Baba amma neman ciyaman dinka karya ne."
@Ophacy ya rubuta:
"Lokacin da Mr Bwala ya ce a ajiye masa wuri a APC wasu daga cikinmu muna tunanin wasa ya ke yi."
Asali: Legit.ng