Kotun Koli Ta Jingine Hukunci Kan Shari'ar Neman Tumbuke Gwamnan Arewa, NNPP Na Cikin Matsala
- Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Taraba da ake takaddama a kai a yau Laraba
- Kotun da ke zamanta a Abuja ta tanadi hukunci kan shari'ar da dan takarar NNPP, Farfesa Sani Yahaya ke kalubalanta
- A baya Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Agbu Kefas na jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Koli ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Taraba a Arewacin Najeriya.
Kotun da ke zamanta a Abuja ta tanadi hukunci kan shari'ar da dan takarar NNPP, Farfesa Sani Yahaya ke kalubalanta.
Wane hukunci kotun ta yanke a shari'ar Taraba?
Alkalan kotun guda biyar da Mai Shari'a, Kudirat Kekere-Ekun ke jagoranta sun bayyana hakan bayan sauraran korafe-korafen dukkan bangarorin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu daukaka karar na neman kotun ta rusa zaben Gwamna Agbu Kefas na jam'iyyar PDP a zaben da aka gudanar a watan Maris.
Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Agbu Kefas a matsayin halastaccen zababben gwamna a jihar, cewar Vanguard.
Hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yi a baya?
Kotun ta ce babu wata hujja da aka gabatar da za ta rusa hukuncin kotun kararrakin zaben gwamnan jihar.
Har ila yau, kotun ta ce ba ta gamsu da korafin NNPP cewa an saba dokar zaben ba inda ta ke bukatar soke zaben, cewar Leadership.
Tun farko, hukumar zabe mai zaman kanta ta ayyana Gwamna Agbu Kefas a matsayin wanda ya lashe zaben a watan Maris.
Kotu ta yi hukunci kan shari'ar zaben Taraba
A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Taraba da ake ta takaddama a kai.
Kotun da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da nasarar Gwamna Agbu Kefas na jam'iyyar PDP a zaben da aka gudanar a watan Maris.
Har ila yau, ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar NNPP, Farfesa Sani Yahaya da ke kalubalantar zaben.
Asali: Legit.ng