Bayan Ya Koma Kano, Gwamna Abba Ya Faɗi Mutum 1 da Ya Cancanci Yabo Kan Hukuncin Kotun Ƙoli
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara jinjinawa Bola Ahmed Tinubu kan hukuncin kotun ƙoli a ƙarar zaben Kano
- Abba ya ayyana shugaban ƙasa a matsayin wanda ya ceci demokuraɗiyya, wanda a cewarsa ba a san halin da Kano zata shiga ba
- Ya kuma ƙara yabawa mazauna Kano da suka fito kwansu da kwarkwata suka tarbe su bayan nasarar da suka samu a kotun koli
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yabawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa basirar da ya nuna wajen kare dimokradiyyar Najeriya.
Gwamnan wanda ya fi shahara da Abba Gida-Gida ya yi wannan furuci ne biyo bayan hukuncin kotun koli, wanda ya tabbatar masa da kujerar gwamnan Kano, The Nation ta tattaro.
Yayin da dubbanin al'umma suka tarbe shi a birnin Kano, Abba ya ce Tinubu ya jurewa matsin lambar wasu ɗaiɗaikun mutane kana ya tsaya kai da fata kan zabin da talakawa suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya ce martabar bangaren shari’a ta kara daukaka a idon jama'a bayan hukuncin kotun koli na soke korarsa da kotun daukaka kara da kotun zaɓe suka yi.
A cewarsa, wasu ɗai-ɗaikun mutane sun yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen sauya muradin al'ummar jihar Kano amma Allah bai ba su nasara ba.
Abba ya yabawa alƙalan kotun koli
Bisa haka gwamnan ya yaba wa alkalan kotun koli (JSCs) da suka yi adalci a hukuncin da suka yanke, wanda hakan ya hana jihar fuskantar “halin da ba a taba tsammani ba.”
“Muna gode wa alkalan da suka yanke hukuncin, domin ba don adalcin hukuncin da suka yanke ba, da ba mu san abin da zai faru ba. Hukuncin ya wanke su."
Ya bayyana cewa al’ummar Kano sun mika godiyar su ga shugaban kasa kan yadda ya kare dimokuradiyya a jihar da ke Arewa maso Yamma.
Gwamna Yusuf ya ci gaba da cewa:
"Na yi matuƙar farin ciki ganin yadda jama'a suka yi tururuwar zuwa tarbar mu, suka yi tattakin awanni takwas kafin ƙarisowa wannan wurin."
"Ba za mu baku kunya ba, ƙofofinmu a buɗe suke, za mu samar da ribar dimokuradiyya ta fannin ilimi, lafiya, tallafawa da dai sauransu.”
Kotun koli zata raba gardama a zaben Kebbi
A wani rahoton kuma kotun koli ta shirya yanke hukunci kan taƙaddamar zaben gwamnan jihar Kebbi wanda aka yi a watan Maris, 2023.
A zaman ranar Talata, 16 ga watan Janairu, 2024 kotun ta tanadi hukunci bayan kammala sauraron kowane ɓangare da shari'ar ta shafa.
Asali: Legit.ng