Gwamnan APC Ya Gaji da Munafurci, Ya Shirya Yin Garambawul a Gwamnatinsa, Ya Fadi Dalili

Gwamnan APC Ya Gaji da Munafurci, Ya Shirya Yin Garambawul a Gwamnatinsa, Ya Fadi Dalili

  • Kasa da wata daya bayan rasuwar gwamnan jihar, sabon gwamna na shan matsin lamba kan yin garambawul a gwamnati
  • Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya yi shirin yin garambawul a gwamnatinsa nan ba da jimawa ba
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Ebenezer Adeniyan ya fitar a Akure

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya shirya yin garambawul a mukaman gwamnatinsa don kawo sauyi a mulki.

Gwamnan wanda ya gaji kujerar bayan rasuwar Rotimi Akeredolu ya bayyana haka a jiya Litinin 15 ga watan Janairu.

Gwamnan APC ya shirya yin garambawul a gwamnatinsa bayan hawa karagar mulki
Gwamna Lucky Aiyedatiwa zai yi garambawul a gwamnatinsa. Hoto: Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Mene Gwamna Lucky ke cewa kan garambawul?

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya karbi rantsuwar kama aiki karo na biyu a gaban jiga-jigai, bayanai sun fito

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Ebenezer Adeniyan ya fitar a Akure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeniyan ya ce gwamnan ya fara shirye-shiryen kawo sauyi a gwamnatin don zabar wasu idan lokacin ya yi, cewar The Guardian.

Ya ce:

"Mai girma Gwamna zai nada mukamai a gwamnatin don inganta rayuwar al'ummar jihar.
"Baya saurin daukar matakin saboda yanzu ya na wadanda suke taimaka masa don zabo wasu masu inganci."

Wane shiri Gwamna Lucky ke yi a Ondo?

Ya kara da cewa:

"Yanzu haka ya na ganawa da masu ruwa da tsaki, ina tabbatar muku idan lokacin ya yi zai gabatar da su."

Daily Trust ta tattaro cewa wannan garambawul din na zuwa ne bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu a ranar 27 ga watan Disamba a Jamus.

Gwamna Aiyedatiwa na fuskantar matsin lamba kan ya yi garambawul a gwamnatinsa yayin da ake fuskantar zaben gwamnan jihar a watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Kano: Bayan nasara a kotu, Gwamnatin Kano ta magantu kan masu niyyar wawushe asusun jihar

Tinubu ya magantu kan yin garambawul a gwamnatinsa

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya yi martani kan jita-jitar cewa zai yi garambawul a gwamnatinsa musamman kujerun Ministoci.

Tinubu ya ce wannan wani abu ne wanda idan lokacin ya yi ba zai buya ba inda ya yi fatali da jita-jitar.

Wannan na zuwa ne bayan zargin samun badakalar makudan kudade ma'aikatar jin kai da walwala da sauran zarge-zarge a gwamnatin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.