Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Gwamnan Arewa, APC Na Tsaka Mai Wuya

Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Gwamnan Arewa, APC Na Tsaka Mai Wuya

  • A karshe kotun koli ta shirya yanke hukunci kan taƙaddamar zaben gwamnan jihar Kebbi wanda aka yi a watan Maris, 2023
  • A zaman ranar Talata, 16 ga watan Janairu, 2024 kotun ta tanadi hukunci bayan kammala sauraron kowane ɓangare da shari'ar ta shafa
  • Ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Aminu Bande, ne ya ɗaukaka kara zuwa gaban kotun koli, yana neman a tsige Gwamna Idris na APC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ƙolin Najeriya ta tanadi hukunci kan ƙarar da aka nemi tsige gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kwamitin alƙalai biyar karkashin jagorancin mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun, ne ya bayyana haka a zaman sauraron ƙarar ranar Talata, 16 ga watan Janairu, 2024, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Uba Sani da sauran cikakken jerin gwamnonin da Kotun Koli za ta yanke hukunci kan nasararsu

Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris.
Kotun koli ta tanadi hukunci a ƙarar da ta nemi tsige Gwamma Idris na jihar Kebbi Hoto: Nasir Idris
Asali: Twitter

Kotun ta tanadi hukuncin ne bayan lauyoyin kowane ɓangare sun gama bayani na ƙarshe, ta ce za a sanar da ranar yanke hukunci nan ba da daɗewa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan takarar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Kebbi da ya gabata ranar 18 ga watan Maris, 2023, Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya ne ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli.

A ƙarar da ya shigar, ya roƙi kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da kotun zaɓe, waɗanda suka tabbatar da nasarar Gwamna Nasir Idris.

Yadda shari'ar ta faro tun a farko

Tun da farko dai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana Ƙauran Gwandu, ɗan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi.

Amma jam'iyyar PDP da ɗan takararta suka nuna rashin gamsuwa da sakamakon, inda suka garzaya kotun sauraron ƙararrakin zaɓe domin neman adalci.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya shirya liyafa bayan nasara a kotun koli, ya aike da muhimmin saƙo ga Bola Tinubu

Sai dai kotun ta kori ƙarar tare da tabbatar da nasarar Gwamna Idris, duk da haka masu ƙarar ba su hakura ba suka wuce kotun ɗaukaka ƙara, wadda ta tabbatar da hukuncin.

Gwamna Nwifuru ya godewa shugaban ƙasa

A wani rahoton na daban Gwamnan Ebonyi ya aike da saƙo na musamman ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bayan samun nasara a kotun koli.

A wurin wata liyafar murna ranar Lahadi, Gwamna Nwifuru ya tabbatarwa al'ummar jihar cewa zai musu hidima cikin gaskiya da ƙauna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262