Wata sabuwa: Hadimin Gwamna Ya Fusata, Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP Kan Matsala 1 Tak
- Tsohon hadimin marigayi gwamnan jihar Ondo kan harkokin midiya, Allen Sawore ya fice daga jam'iyyar PDP
- Babban jigon siyasar ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne saboda zaben gwamna na ƙaratowa kuma rikici ya yi yawa a PDP
- A cewarsa lokaci ya yi da zai sauya akalar siyasarsa, yana mai gode wa PDP bisa damarmakin da ta ba shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ondo - Tsohon mataimaki na musamman ga marigayi gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu kan harkokin midiya, Allen Sowore, ya fice daga jam’iyyar PDP.
Sowore, ya kasance tsohon mai bai wa tsohon mataimakin gwamna shawara, Agboola Ajayi, kuma daraktan yada labarai na shiyyar Ondo ta kudu a zaben 2023, Vanguard ta ruwaito.
Meyasa ya fice daga jam'iyyar PDP
Tsohon hadimin gwamnan ya bayyana cewa ya ɗauki matakin barin jam'iyyar PDP ne saboda rigingimun cikin gida da suka dabaibayeta a jihar Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Sawore ya tabbatar da sauya sheƙa daga PDP ne a wata wasiƙa da ya aike wa shugaban jam'iyyar na gunduma ta II Apoi, ƙaramar hukumar Ese-Odo.
A cewarsa, ya yanke shawarar ne sakamakon zaben gwamna da ke ƙaratowa da kuma rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
A cikin wasikar wacce ya yi wa taken “Ficewa daga jam’iyyar PDP” ya ce:
"Na rubuto muku wannan takarda ne domin sanar da ficewa ta daga jam'iyyar PDP a hukumance. Na yanke wannan shawar ne duba da zaben gwamna mai zuwa a Ondo.
"Bayan dogon nazari a tsanake, na fahimci cewa lokaci ya yi da zan sauya akalar siyasata. Wannan sauyi ya samo asali ne daga rigingimun cikin gida da ya taɗiye jam’iyyar PDP, wanda ke matukar damuna.
"Na yaba muku bisa fahimtar matakin da na ɗauka, ina kuma miƙa godiyata bisa damarmaki da gogewar da na samu tsawon lokacin da na kasance a PDP."
An lalata motar kamfe a Edo
A wani rahoton kuma wasu mahara sun yi kaca-kaca da motar kamfen mataimakin gwamnan jihar Edo kuma ɗan takarar gwamna a PDP, Philip Shaibu.
Kodinetan kamfen Shaibu ya bayyana cewa lamarin ya auku ne jim kaɗan bayan sun gama taro a Ekpoma.
Asali: Legit.ng