Ganduje Ya Gamu da Rudanin Takarar Farko a APC Tun Bayan Zama Shugaban Jam’iyya

Ganduje Ya Gamu da Rudanin Takarar Farko a APC Tun Bayan Zama Shugaban Jam’iyya

  • Nasarar Ifeoluwa Ehindero a zaben tsaida gwani da APC ta shirya a mazabar Akoko yar bar baya da kura
  • Olugbenga Araoyinbo ya ce sam ba zai karbi sakamakon zaben da aka yi ba, ya ce an sabawa ka’idojin jam'iyya
  • ‘Dan siyasar ya roki Abdullahi Umar Ganduje su sake shirya wani zaben tsaida ‘dan takara na dabam a APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Ondo - Abubuwa sun balbalcewa jam’iyyar APC a game da zaben tsaida gwanin ‘dan takara a mazabar Akoko a jihar Ondo.

Daily Trust ta ce nasarar da Ifeoluwa Ehindero ya samu wajen lashe tikitin takarar ‘dan majalisar Akoko ya haifar da rikici.

Ganduje
APC NWC ta karbi korafin takarar Majalisa Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, House of Representatives
Asali: Facebook

Ifeoluwa Ehindero wanda yaro ne a wajen tsohon Sufetan ‘yan sanda na kasa watau Sunday Ehindero ne ya karbi tutan APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya warware abin da Ganduje ya so a shiryawa Kano a Kotun Koli Inji Abba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana neman agajin Ganduje a APC

Olugbenga Araoyinbo ya ruga wajen shugabannin APC na kasa, yana neman a ayyana shi a matsayin wanda ya ci zaben gwani.

Jam’iyya mai mulki ta shirya zaben fitar da ‘dan takara ne domin maye gurbin Olubunmi Tunji Ojo wanda ya zama minista a yau.

Kafin yanzu Hon. Tunji Ojo ne ya wakilci mutanen Akoko ta Arewa maso yamma da Akoko ta Arewa maso gabas a majalisar wakilai.

Ifeoluwa Ehindero zai samu tikitin APC?

Da aka shirya zabe, APC ta ce Ifeoluwa Ehindero ya tashi da kuri’u 105 a cikin 106.

Daily Post ta ce Araoyinbo bai gamsu da zaben da aka shirya ba, ya fadawa Abdullahi Ganduje an yi watsi da doka da tsarin APC.

A korafin da ya gabatar gaban majalisar NWC da Ganduje yake jagoranta, ‘dan siyasar ya zargi ‘yan jam’iyyarsa da yin karfa-karfa.

Kara karanta wannan

Jam’iyyun adawa sun cigaba da shirin hada kai domin yakar Tinubu da APC a 2027

Makomar APC a zaben Akoko

A cewar Araoyinbo, ba mutanen da ‘yan APC na reshen Akoko su ke so aka tsaida ba, don haka ya bukaci a shirya wani sabon zabe.

Har ila yau, Araoyinbo ya roki shugaban APC na kasa ya hana maganar ta je kotu, ya ce hakan zai kawo masu matsala wajen takara.

Ya aka yi Tinubu ya samu mulki a APC?

A makon da ya wuce, an ji labari Femi Gbajabiamila ya fadi yadda aminan Bola Tinubu suka yi sanadiyyar zamansa shugaban kasa.

Tsohon shugaban majalisar wakilan ya ce wadanda su kayi aiki da Bola Tinubu a 1992 sun yi masa rana da aka zo yin zabe a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng