Ministan N/Delta ya bayyana masu cin kwangilolin NDDC bayan barazanar NASS

Ministan N/Delta ya bayyana masu cin kwangilolin NDDC bayan barazanar NASS

A karshe Ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio ya fito ya maidawa Majalisar wakilan tarayya martani sakamakon kalubalen da aka jefa masa.

Sanata Godswill Akpabio a wata takarda ya ambaci sunan Sanatoci hudu da ya ce sun karbi kwangiloli 74 daga ma’aikatar NDDC daga shekarar 2017 zuwa yanzu.

Hakan na zuwa ne bayan majalisar wakilan ta ba ministan wa’adin kwana biyu ya fadi sunayen ‘yan majalisar da su ke samun kwangilar a ma’aikatar ta Neja-Delta.

Majalisa ta nuna cewa za ta garzaya kotu da Ministan Neja-Deltan ganin wa’adin da aka ba sa ya kare ba tare da ya gabatar da sunayen yan majalisar da suke samun kwangilar ba.

A karshen makon nan, Ministan ya turawa majalisa takarda mai kunshe da jerin Sanatocin da NDDC ta ba kwangiloli, daga ciki akwai Sanata Peter Nwaobosh wanda aka ba kwangiloli 43.

Takardar ta ce an ba Sanata Matthew Urhoghide, James Manager da kuma Sanata Sam Anyanwu kwangiloli 21 duk daga shekarar 2017 zuwa yanzu.

Amma sai dai Sanata Nwaoboshi ya yi maza ya karyata wannan zargi, ya kira Akpabio da rikitaccen mutumi kamar yadda jaridar This Day ta rahoto a ranar Litinin.

KU KARANTA: Sojoji sun kashe Biliyoyi wajen sayen makamai a Najeriya

Ministan N/Delta ya bayyana masu cin kwangilolin NDDC bayan barazanar NASS
Godswill Akpabio Hoto: NASS
Asali: UGC

Peter Nwaobosh ya kalubalanci Ministan ya fadi sunan kamfaninsa da ya yi wannan aiki da kuma sunayen Darektocin kamfanin, Nwaobosh ya ce bai neman kwangilolo.

A takardar da ta fito daga ofishin Ministan, an ambaci wasu kwangilolin gyara hanyoyin lshu Ani Ukwu, Issele Uku, titin ldumuogbe, titin Otolokpo a matsayin ayyukan da aka ba Nwoboshi.

Akpabio ya ce Mathew Urhoghide ya samu kwangiloli shida, haka James Manager ya samu kwangiloli shida daga hannun ma’aikatar NDDC.

Tsohon Sanata Sam Anyanwu ne ake zargin ya samu kwangiloli 19 a lokacin da ya ke majalisa.

Bayan nan Ministan ya zargi shugaban kwamitin NDDC a majalisar wakilai, Honarabul Olubunmi Tunji-Ojo da cusa kwangiloli 19 na Naira biliyan 9 a cikin kasafin kudin NDDC.

Tunji-Ojo ya musanya wannan zargi, ya ce bai cusa wasu ayyuka a cikin kundin kasafin shekarar 2019 ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel