Gwamnan Arewa Ya Bayyana Babban Abin da Ya Ke Mutunta Tinubu da Shi Bayan Hukuncin Kotun Koli
- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi martani kan irin halin kirki na Shugaba Tinubu bayan yanke hukunci
- Gwamnan ya ce Tinubu ya na da matukar girma a wurinshi ganin yadda ya kau da kai a shari'ar zaben jihohi.
- Wannan na zuwa ne bayan nasarar da gwamnan ya samu a Kotun Koli a jiya Juma'a 12 ga watan Janairu a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana irin yadda ya ke kallon Shugaba Tinubu a zuciyarshi.
Gwamnan ya ce Tinubu ya na da matukar girma a wurinshi ganin yadda ya kau da kai a shari'ar zaben jihohi.
Mene Kaura ke cewa kan Tinubu?
Ya ce Tinubu ya tabbatar da cewa shi mai bin doka ne da kuma nuna kishin kasa baki daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya yi nasara a Kotun Koli a jiya Juma'a 12 ga watan Janairu, cewar Leadership.
Bala ya ce wasu 'yan siyasa a jihar sun yi ta kokarin hada shi da Shugaba Tinubu yayin da ake shirin yanke hukunci.
A cewarsa:
"Shugaba Tinubu mutum ne mai mutunta dokar kasa wanda ya cancanci a kwaikwaye shi."
Gargadin Kaura ga masu sharri
Gwamnan ya kara da cewa babu wani abin da zai durkusar da su duk girman shirin makirci da aka yi.
Gwamna Kaura ya ce wannan nasara da ya samu ya kara saka masa amincewa da bangaren shari'ar kasar, NAN ta tattaro.
Ya ce zai yi duk mai yiyuwa don ganin ya inganta rayuwar jama'ar jihar Bauchi wurin kawo abubuwan more rayuwa.
Ya kara da cewa:
"Na sani mutane su na cikin yunwa da bacin rai, amma a Bauchi abin da sauki saboda irin matakan da mu ka dauka."
Gwamna Abba Kabir ya gode wa Tinubu
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya yi martani bayan yanke hukuncin Kotun Koli a jiya.
Abba yayin martanin ya godewa Shugaba Tinubu kan irin fage da ya bayar wurin tabbatar da an yi adalci a hukuncin.
Har ila yau, Gwamnan ya godewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da sauran 'yan jihar Kano.
Asali: Legit.ng