Hukuncin Kotun Koli Kan Zaben Kano: Kwankwaso Ya Magantu, Ya Aika Sako Ga Yan Najeriya

Hukuncin Kotun Koli Kan Zaben Kano: Kwankwaso Ya Magantu, Ya Aika Sako Ga Yan Najeriya

  • Shugabannin jam'iyyar NNPP na murna kan sakamakon hukuncin Kotun Koli da ya kai nasara bangaren dan takararsu kuma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
  • Legit Hausa ta rahoto cewa Kotun Koli ta soke hukuncin kotun daukaka kara, wanda ya tsige Gwamna Yusuf daga kujerarsa
  • Babban jagoran jam'iyyar NNPP. Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna gamsuwa da hukuncin babbar kotun kasar

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kano, jihar Kano - Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023, ya bayyana cewa shari'ar zaben gwamnan jihar Kano darasi ne ga kowa.

Kwankwaso ya yi jawabi kan hukuncin kotun koli a zaben gwamnan Kano
Hukuncin Kotun Koli Kan Zaben Kano: Kwankwaso Ya Magantu, Ya Aika Sako Ga Yan Najeriya Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Facebook

Kwankwaso, wanda ya kasance ubangidan Gwamna Abba Kabir Yusuf a siyasa, ya ce hukuncin Kotun Kolin ya dawo da muradin mutanen jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya cimma yarjejeniya da Tinubu kan shari'ar zaben gwamnan Kano? Gaskiya ta bayyana

Tsohon gwamnan kuma sanata ya roki yan siyasa da su yi kokarin cin zabe ta hanyar akwatunan zabe ba ta bayan fage ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya ce:

"Mun gode Allah cewa Kotun Koli ta dawo da fatan mutanen.
"Takaddamar zaben gwamnan jihar Kano na 2023 darasi ne gare mu gabaki daya."

Jigon PDP ya yi hasashe kan Abba da Kwankwaso

A wani labarin, mun ji cewa Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar, wani mamba a jam'iyyar PDP, ya yi hasashen cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ubangidansa a siyasa, Rabiu Kwankwaso, za su sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Abubakar, darakta janar na kungiyar Atiku, ya wallafa hakan ne a shafinsa na X a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu, bayan Kotun Koli ta soke hukuncin da ya tsige Gwamna Yusuf daga kujerarsa.

Kara karanta wannan

"Ta karewa Ganduje": Jigon PDP ya yi hasashen mataki na gaba da gwamnan Kano zai dauka bayan nasara

Gawuna ya yi martani kan kayen da ya sha

A gefe guda kuma, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Kano, ya ce ya amince da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan shari'ar gwamnan jihar a matsayin hukuncin Allah.

Gawuna ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da jaridar BBC Hausa.

Gawuna da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar New Nigeria People's Party (NNPP) sun yi ta shari'a bayan zaɓen gwamna a watan Maris na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng