Bayan Hukuncin Kotun Koli Shugaba Tinubu Ya Fadi Muhimmin Abu 1 da Yake So Gwamnonin APC Su Yi
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da su tashi tsaye
- Shugaban ƙasar ya buƙace su da su dage damtse wajen ganin sun jawo ƴan adawa cikin jam'iyyar ta APC
- Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci gwamnonin da su samar tare da aiwatar da manufofi waɗanda za su taimaki ƴan Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya shaidawa gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da su jajirce su jawo ƴan adawa zuwa cikin jam'iyyar.
Tinubu ya ce jawo ƴan adawan zai taimaka wajen samun waraka da kuma haɗa kan ƙasar nan domin cimma burin ƙasa baki daya.
Shugaba Tinubu ya koka da cewa ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da al’ummar ƙasar ke fuskanta shi ne rarrabuwar kawuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane kira Tinubu ya yi ga gwamnonin APC?
Don haka, Tinubu ya roƙi gwamnonin da aka zaba a ƙarƙashin APC da su tsara da aiwatar da manufofin da suka bai wa ƴan Najeriya fifiko.
Ya buƙace su da su riƙa la’akari da maslahar ƙasa sama da alaƙa da siyasa.
Shugaban ƙasan ya yi waɗannan buƙatun ne lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin ƙungiyar gwamnonin APC a fadar gwamnati da ke Abuja.
Sai dai ya ce dole ne jam’iyyar da ke mulki ta yi ƙoƙari wajen ganin an samu waraka da haɗa kan ƙasa.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Cif Ajuri Ngelale ya fitar da sanarwa kan taron.
Tinubu ya faɗawa gwamnonin APC cewa:
"Kuna iya canja mutane. Kuna iya kira ga mutane su zo gare ku."
Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Kan Hukuncin Kotun Ƙoli
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta mayar da martani ga hukuncin kotun koli kan kararrakin zaben gwamnoni da ta yanke ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu.
Jam’iyyar mai mulki ta yaba da hukunce-hukuncen da kotun kolin ta yanke, tana mai bayyana hakan a matsayin tabbatar da cewa shari’a ɓangare ne mai cin gashin kansa.
Asali: Legit.ng