Jam'iyyar APC Ta Maida Martani Kan Nasarar Gwamna Abba Na Kano da Wasu Gwamnoni a Kotun Ƙoli

Jam'iyyar APC Ta Maida Martani Kan Nasarar Gwamna Abba Na Kano da Wasu Gwamnoni a Kotun Ƙoli

  • Jam'iyyar APC ta yabawa kotun koli bisa hukunce-hukuncen da ta yanke a ƙararrakin zaben gwamnonin da aka yi a watan Maris
  • APC mai mulki ta bayyana cewa hukuncin da kotun kolin ta yanke ya ƙara nuna tabbacin cewa ɓangaren shari'a na cin gashin kansa
  • Kakakin jam'iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya roƙi babbar jam'iyyar adawa PDP ta nemi yafiyar alkalai bisa sukar da ta musu a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta mayar da martani ga hukuncin kotun koli kan kararrakin zaben gwamnoni da ta yanke ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu.

Jam’iyyar mai mulki ta yaba da hukunce-hukuncen da kotun kolin ta yanke, tana mai bayyana hakan a matsayin tabbatar da cewa shari’a ɓangare ne mai cin gashin kansa.

Kara karanta wannan

Atiku ya faɗi shirinsa na gaba kan Tinubu da APC bayan gwamnoni 4 sun yi nasara a kotun ƙoli

Gwamnan Abba Kabir da Celeb Mutfwang.
Jam'iyyar APC Ta Maida Martani da Hukuncin Kotun Koli Kan Zaben Kano da Wasu Jihohi Hoto: Abba Kabir Yusuf, Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Kakakin jam’iyyar APC, Felix Morka, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta shafin jam'iyyar na manhajar X (wanda aka fi sani da Twitter).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Morka ya ce APC ta yi maraba da hukuncin kotun koli a shari’o’in jihohin Legas, Ebonyi da Kuros Riba, inda ta tabbatar da nasarar Babajide Sanwo-Olu, Francis Nwifuru, da Bassey Otu.

Sai dai kotun ta soke hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan gwamnonin PDP, Dauda Lawal na jihar Zamfara, da Celeb Mutfwang na Filato, da na NNPP, Abba Yusuf na Kano.

Martanin APC kan hukuncin kotun koli

Kakakin APC ya ce:

"Duk da hukuncin kotun kolin zai haddasa cece kuce da ra'ayoyi mabanbanta amma shi ne na ƙarshe kuma raba gardama. Hukuncin yau ya ƙara tabbatar da ƙarfin iko da cin gashin kan sashin shari'a."

Kara karanta wannan

Kotun koli ta ƙara yanke hukunci kan sahihancin nasarar gwamnan adawa, PDP ta yi warwas

Jam’iyyar APC mai mulki ta kuma caccaki PDP, inda ta yi kira ga ‘yan adawa da su nemi afuwar alkalai bisa suka da kalamai marasa daɗi da suka jefa wa ɓangaren shari'a.

Atiku ya fara shirin kayar da Tinubu a 2027

A wani rahoton kuma Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana matakin da zai ɗauka kan APC da Shugaba Tinubu a 2027.

Atiku ya ce ya kudiri aniya tare da shirya jagorantar gamayyar jam'iyyun adawa da zasu kawar da APC da Tinubu daga kan mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262