Kai Tsaye: Shari'ar Zaben Gwamnonin Jihohin Bauchi da Zamfara Ke Gudana

Kai Tsaye: Shari'ar Zaben Gwamnonin Jihohin Bauchi da Zamfara Ke Gudana

Rana bata karya sai dai uwar diya ta ji kunya! A yau ne Kotun Koli za ta zartar da hukuncin karshe kan takkadamar zabukan gwamnoni da aka yi a ranar 18 ga watan Maris din 2023.

Daga cikin shario'in gwamnoni da Kotun Kolin za ta yi hukunci kansu a yau Juma'a, 12 ga watan Janairu, harda na jihohin Bauchi da Zamfara.

Kasance tare da Legit Hausa don jin yadda zaman hukuncin ke gudana kai tsaye.

Kotu ta tabbatar da nasarar Mohammed matsayin gwamnan Bauchi

Rahotan da Legit Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa Kotun Koli ta tabbatar da nasarar zaben Bala Mohammed matsayin gwamnan jihar Bauchi, rahoton The Cable.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da APC da dan takararta Sadique Abubakar suka shigar na kalubalantar hukuncin Kotun Daukaka Kara da na kotun sauraron kararrakin zaben jihar

An fara sauraran shari'ar zaben jihar Bauchi

Bayan yanke hukunci kan shari'ar gwamnan jihar Legas, Kotun Koli ta fara karanta shari'ar gwamnan Bauchi.

Jam'iyyar APC da dan takarar ta Sadique Abubakar ne suka shigar da karar, inda suke so kotun ta ruguza zen jihar da ya ba Gwamna Bala Mohammed nasara.Bayan yanke hukunci kan shari'ar gwamnan jihar Legas, Kotun Koli ta fara karanta shari'ar gwamnan Bauchi. Jam'iyyar APC da dan takarar ta Sadique Abubakar ne suka shigar da karar, inda suke so kotun ta ruguza zen jihar da ya ba Gwamna Bala Mohammed nasara. Bayan yanke hukunci kan shari'ar gwamnan jihar Legas, Kotun Koli ta fara karanta shari'ar gwamnan Bauchi. Jam'iyyar APC da dan takarar ta Sadique Abubakar ne suka shigar da karar, inda suke so kotun ta ruguza zen jihar da ya ba Gwamna Bala Mohammed nasara.

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.