Yan Najeriya Sun Yi Martani Yayin da Kotun Koli Ke Hukunci a Zabukan Gwamnonin Kano, Filato da Legas

Yan Najeriya Sun Yi Martani Yayin da Kotun Koli Ke Hukunci a Zabukan Gwamnonin Kano, Filato da Legas

  • Kotun Kolin Najeriya za ta yanke hukuncin karshe kan takaddamar zabukan gwamnoni guda takwas a yau Juma'a, 12 ga watan Janairu
  • Yayin da ake dakon jin yadda za ta kaya a kotun, yan Najeriya sun garzaya shafukan soshiyal midiya domin tofa albarkacin bakunansu
  • Yayin da wasu suka bayyana wadanda suke so su yi nasara a Kotun, wasu sun ja hankalin al'umma da su karbi sakamakon hukuncin a duk yadda ya zo

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yan Najeriya sun shiga zullumi yayin da Kotun Koli ke shirin yanke hukunci kan zabukan gwamnoni na ranar 18 ga watan Maris, 2023, a yau Juma'a, 12 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban NNPP ya faɗi gaskiyar wanda zai samu nasarar tsakanin Abba da Gawuna a kotun koli

Johohin da Kotun Kolin za ta yanke hukunci kansu sun hada da Kano, Filato, Legas, Zamfara, Cross Rivers, Bauchi da Ebonyi.

Yan Najeriya sun yi martani gabannin hukuncin kotun koli
Yan Najeriya Sun Yi Martani Yayin da Kotun Koli Ke Hukunci a Zabukan Gwamnonin Kano, Filato da Legas
Asali: Twitter

Me yan Najeriya ke cewa?

Bashir Ahmad, @BashirAhmaad, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wallafa a dandalin X:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yayin da Kotun Koli za ta yanke hukuncinta a gobe, Juma'a, ina aika sakon fatan alkhairi ga mai girma Dr. Nasir Yusuf Gawuna. Ina rokawa jam'iyyarmu nasara sannan, abu mafi muhimmanci, don ci gaban jiharmu mai albarka, Kano da mutanenta."

Muräd Faïsaal, @elfaisaal, ya ce:

"Zan shawarci mutanena yan #Kwankwasiyya people da kada su jefa rayuwarsu cikin hatsari, idan abubuwa suka yi kudu a Kotun Koli a yau.
"Sai muna raye ne za mu yi faftuka don wata rana. Yau ba shine karshe ba. Allah zai sake ba mu damar yi wa mutanenmu hidima. Don Allah mu sanya Kano a gaba."

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Abba Gida-Gida da wasu gwamnoni 3 sun isa Kotun Koli gabannin yanke hukunci

jœy shèkwônúzhïbó, @joeyzhibo, ya ce:

"Ya ke jihar Filato;
"Duk abun da Kotun Koli ta zartar a yau, mu amshi sakamakon sannan mu ci gaba da harkokinmu."

YaronMalan, @AbdulhamidYaro4, ya ce:

"Mutanen jihar Zamfara sun zabi Gwamna @daudalawal_Allah kada ya ba Kotun Koli damar canja muradin mutanen..."

Sanwo-Olu ya tabbata Gwamnan Legas

A wani labarin kuma, mun ji cewa Kotun Kolin Najeriya a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu, ta tabbatar da zaben Babajide Sanwo-Olu a matsayin zababben gwamnan jihar Legas.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Maishari'a Garba Lawal wanda ya karanto hukuncin ya yi watsi da karar da Gbadebo Rhodes-Vivour na jam'iyyar LP ya shigar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng