Dalilin da Ya Sa Ganduje Zai Gina Babban Coci a Sakatariyar APC da Ke Abuja
- Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam'iyyar APC na kasa ya ce ginin coci a harabar sakatariyar jam'iyyar ya kankama
- Ya bayyana cewa gina cocin zai kawo dai daito tsakanin mabiya addinin Muslunci da Kirista wajen gudanar da ibadojin su
- Ganduje ya kuma sha alwashin jawo karin yawan gwamnoni da 'yan majalisu zuwa jam'iyyar APC kafin shekarar 2024 ta kare
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fadi dalilin da ya sa zai gina babban coci a harabar sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja.
Da ya ke jawabi yayin kai ziyara don ganin yadda ginin cocin ke gudana, ya ce hakan zai ba Kiristoci damar yin ibadar su a sakatariyar kamar yadda Musulmi ke yi.
Ayyukan da muke yi a harabar sakatariyar APC - Ganduje
Ganduje wanda ya sha alwashin tabbatar da nasarar APC a matakan kasar ya kuma yi alkawarin bunkasa 'yan jaridar da ke aiki a sakatariyar jam'iyyar, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Kowa ya san babu coci a cikin sakatariyar, amma yanzu mun yi sabuwa coci, saboda kawo dai daito tsakanin mabiya addinin biyu.
"Mun gina shaguna a cikin sakatariyar don haramta tallace-tallace, sannan mun shirya gyara ofishin 'yan jarida ta hanyar saka sabbin kayan aiki na zamani."
APC za ta kara yawan gwamnoni da'yan majalisu a 2024
Arise News ta ruwaito Ganduje na ci gaba da cewa burin jam'iyyar shi ne kara yawan 'yan majalisu a fadin kasar, kuma ya ce za su jawo wasu gwamnoni zuwa jam'iyyar kafin shekara ta kare.
Ya ce:
"Al'ada ce ta wasu jam'iyyu, ba sa aikin komai sai idan zabe ya zo, amma ni zan tabbatar APC ta yi aiki tukuru don kara yawan 'yan majalisu da gwamnoni.
"Hakan zai kara wa jam'iyyar karfi da kuma fadada ayyukan ta a fadin kasar, kuma da hakan ne za mu tabbatar da yunkurin Shugaba Tinubu na samar da sabuwar Najeriya."
Bankin Musulunci zai gina cibiyoyin tara madara 60 a Kano
A wani labarin kuma, bankin cigaban Musulunci (IsDB) tare da asusun inganta rayuwa (LLF) zai gina cibiyoyin tara madara 60 a fadin jihar Kano.
IsDB da LLG za su yi aikin ne karkashin shirin bunkasa noma da makiyaya ta jihar Kano (KSADP), da nufin cike gurbin da ke tsakanin makiyaya da masana'antar sarrafa madarar shanu.
Asali: Legit.ng