Ana Zaman Dar-Dar a Kano Yayin da Ake Daf da Yanke Hukunci, ’Yan Sanda Sun Tura Sako Ga Jama’a
- Ana cikin dar-dar a Kano yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli a gobe Juma'a 12 ga watan Janairu
- Rundunar 'yan sanda a jihar ta ba da tabbacin samar da tsaro a wurare da dama don dakile tashin hankali
- Wannan na zuwa ne yayin da Kotun Koli ta sanya gobe Juma'a a matsayin ranar yanke hukuncin karshe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli a Kano, rundunar 'yan sanda ta tura sakon jan hankali ga jama'a.
Rundunar ta ce ta shirya dakile duk wani shiri na kawo tashin hankali a jihar a gobe juma'a 12 ga watan Janairu, cewar Leadership.
Wane sako 'yan sandan suka tura?
Wannan na zuwa yayin da Kotun Koli ta sanya gobe Juma'a 12 ga watan Janairu a matsayin ranar yanke hukuncin karshe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Hussaini Gumel shi a bayyana haka a yau Alhamis 11 ga watan Janairu yayin ganawa da 'yan jaridu a Kano.
Gumel ya ba da tabbacin cewa za su ba da tsaro kafin da lokacin da kuma bayan sanar da sakamakon shari'ar gwamnan jihar.
Kwamishinan ya ce rundunar ta samar da wani yanayi don bai wa mutane damar gudanar da harkokinsu ba tare da matsala ba, cewar Daily Post.
Tabbacin rundunar 'yan sanda
Ya ce:
"Mun samar da jami'an tsaro a ko ina don samar da tsaro a wasu wurare na musamman.
"Wuraren sun hada da ofisoshin jam'iyyun siyasa da gidan gwamnati da hukumar INEC da bankuna da kasuwanni.
Nesa ta zo kusa: Kotun koli ta sanya ranar yanke hukuncin kan zaben gwamnan Kano, Bauchi da wasu jihohi 5
"Sauran sun hada da wuraren ibada da wuraren shakatawa da tashoshin mota da sauransu."
Ya ce ya ba da tabbaci wa jama'a samun tsaro dari bida dari inda ya bukaci mutane su fita harkokinsu ba tare da wata matsala ba.
Dattawan Kano sun yi magantu an EFCC
A wani labarin, Dattawan jihar Kano sun magantu kan samamen EFCC kan ofishin kamfanin Dangote.
Dattawan suka ce hakan zai ruguza tattalin arzikin kasar da kuma hana masu zuba hannun jari zama.
Asali: Legit.ng