Kujerar Gwamnan APC Na Tangal-Tangal, Kotun Ƙoli Ta Tanadi Hukunci Kan Zaben da Ya Ci a 2023

Kujerar Gwamnan APC Na Tangal-Tangal, Kotun Ƙoli Ta Tanadi Hukunci Kan Zaben da Ya Ci a 2023

  • Kotun koli ta gama sauraron ƙarar da jam'iyyar PDP ta kalubalanci nasarar Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Riba
  • A zaman ranar Alhamis, kotun mai daraja ta ɗaya ta tanadi hukunci wanda ake sa ran za ta yanke ranar Jumu'a mai zuwa
  • PDP da ɗan takararta na gwamna sun yi zargin cewa Gwamna Otu, ɗan takarar APC ya yi amfani da jabun takardu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun kolin Najeriya ta tanadin hukuncinta a karar da ke kalubalantar zaben Gwamna Bassey Otu na jihar Cross River, rahoton Daily Trust.

Kwamitin alƙalai biyar na kotun karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro ne ya tanadi hukuncin ranar Alhamis bayan sauraron kowane bangare na ƙarar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta aike da sako mai muhimmanci yayin da kotun koli ke dab da yanke hukunci

Gwamnan Kuros Riba, Bassey Otu.
Kujerar Gwamnan APC Ta Fara Tangal-Tangal, Kotun Ƙoli Ta Tanadi Hukunci Kan Nasarar da Ya Samu Hoto: Bassey Otu
Asali: Facebook

Sai dai wasu majiyoyi daga kotun kolin sun tabbatar da cewa za a yanke hukunci ranar Juma’a bayan ƙarƙare karanto hukunci a kararrakin zaben gwamnonin jihohin Kano da Filato da Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar gwamnan jihar Cross River na jam’iyyar PDP, Sanata Sandy Onor ne ya shigar da kara, yana kalubalantar nasarar Gwamna Otu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Yadda zaman kotun ya kaya tsakanin ɓangarorin

Da yake bayani a gaban kotun, lauyan jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Joshua Musa (SAN), ya yi zargin cewa Gwamna Otu ya yi amfani da takardun karatu na jabu.

Haka nan kuma ya faɗa wa kotun cewa Gwamnan bai cancanci tsayawa takara a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023 ba.

Amma a nasa ɓangaren lauyan Otu ya ce wadanda suka shigar da karar sun gaza tabbatar da zargin jabun takardu da rashin zama cikakken mamban jam’iyyar APC kan Otu.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan takaddamar zaben gwamnan PDP, NNPP ta gurza kasa

Bisa haka ne lauyan ya buƙaci kotun wacce ake wa taken daga ke sai Allah ya isa ta yi fatali da ƙarar gaba ɗaya.

Ranar Jumu'a, 12 ga watan Janairu, 2024 kotun koli zata bayyana hukunci kan kararrakin zaben gwamnoni akalla bakwai, kamar yadda Channels tv ta tattaro.

Kotu ta bada belin tsohon minista

A wani rahoton kuma Babbar kotun Abuja ta bada belin tsohon ministan wutar lantarki, Olu Agunloye, kan kuɗi Naira miliyan 50 ranar Alhamis.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Mista Agunloye gaban ƙuliya ne kan zargin damfara a kwangilar tashar wutar mambila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262