Nesa Ta Zo Kusa: Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Kan Zaben Gwamnan Kano, Bauchi Da Jihohi 5

Nesa Ta Zo Kusa: Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Kan Zaben Gwamnan Kano, Bauchi Da Jihohi 5

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci a kararrakin da aka shigar gabanta kan zaben gwamnonin jihohi 7 ranar Juma’a, 12 ga Janairu, 2024, daga karfe 9 na safe.

Jihohin sun hada da Legas, Kano, Zamfara, Filato, Ebonyi, Bauchi da kuma Kuros Riba, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kotun koli zata yanke hukunci kan zaben gwamnoni 7.
Kotun koli ta sanya ranar yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano, Bauchi da wasu jihohi 5 Hoto: Supreme Court Of Nigeria
Asali: Facebook

Legit Hausa ta tattaro muku wasu muhimman bayanai game da shari'o'in wasu daga cikin jihohin da zasu san makomarsu idan Allah ya kaimu gobe Jumu'a.

Kano: Abba Vs Gawuna

A karshen watan Disamba, kotun kolin ta tanadi hukunci a karar da Gwamna Abba Yusuf na Kano ya shigar, yana kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da kotun zabe ta jiha.

Kara karanta wannan

Kujerar gwamnan APC na tangal-tangal, kotun ƙoli ta tanadi hukunci kan zaɓen da ya ci a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin allƙalai biyar karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro ya ajiye hukuncin ne bayan da bangarorin suka amince da takaitaccen bayaninsu na ƙarshe.

Gawuna da Gwamna Abba.
Kotun koli ta sanya ranar yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano, Bauchi da wasu jihohi 5 Hoto: Dr Nasir Gawuna, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Tun a watan Satumba, kotun zaɓe ta soke nasarar Yusuf, dan takarar jam'iyyar NNPP a zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga Maris, kana ta ayyana Nasir Gawuna na APC a matsayin gwamnan Kano.

A ranar 13 ga watan Nuwamba, kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da wannan hukunci, inda ta yanke cewa Abba Kabir ba mamban NNPP bane a lokoacin da ya nemi takara.

Filato: Mutfwang VS Goshwe

A ranar 9 ga Janairu, 2024, kotun ƙoli ta tanadi hukunci a karar da gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya shigar, yana neman soke hukuncin Kotun daukaka kara.

Gwamnan ta bakin lauyansa, Kanu Agabi, ya roki kotun da ta tabbatar da hukuncin kotun zaɓe kuma ta yi watsi da hukuncin kotun daukaka kara.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Babbar Kotu ta yanke hukunci kan tsohon ministan da ake zargi da karkatar da $6bn

Lauyan ya shaida wa kotun koli cewa wadanda ake kara ba su da hurumin tsoma baki kan yadda jam’iyya ke zaben shugabanninta na jihohi.

Gwamna Mutfwang da Goshwe.
Kotun koli ta sanya ranar yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano, Bauchi da wasu jihohi 5 Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: UGC

A watan Nuwamba ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta sauke Mutfwang kuma ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta ba Goshwe na APC takardar shaidar cin zabe.

Zamfara: Lawal VS Matawalle

Dauda Lawal na babbar jam'iyyar adawa PDP ya lashe zaɓen gwamnan jihar Zamfara ranar 18 ga watan Maris, 2023, wanda ya ba shi damar sauke gwamna mai ci, Bello Matawalle na APC.

Matawalle, wanda yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaro, ya zargi INEC da dakushe nasararsa ta hanyar kin sanya sakamakon zaben wasu gundumomi.

A farko, kotun zabe ta kori ƙarar Matawalle bisa rashin cancanta kana ta tabbatar da nasarar Gwamna Lawal tare da cin tarar masu shigar da ƙara N500,000.

Dauda Lawal da Bello Matawalle.
Nesa ta zo kusa: Kotun koli ta sanya ranar yanke hukuncin kan zaben gwamnan Kano, Bauchi da jihohi 5 Hoto: Dauda Lawal, Bello Matawalle
Asali: Twitter

Bayan dan takarar APC ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara, mai shari'a Sybil Nwaka, ya tsige Lawal kana ya umarci INEC ta shirya zabe a runfunan da ba a haɗa da su ba a baya.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan takaddamar zaben gwamnan PDP, NNPP ta gurza kasa

Amma gwamnan bai gamsu da wannan hukunci ba, shiyasa ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli, wanda zata raba gardama gobe.

Bauchi: Mohammed VS Abubakar

Hakazalika, a watan Nuwamba, kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi a zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga Maris.

Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Sadique Abubakar, ya shigar da karar ne biyo bayan hukuncin kotun sauraron kararrakin zaɓe wadda ta tabbatar da nasarar Ƙauran Bauchi.

Duk da rashin nasara, dan takarar APC bai haƙura ba ya sake ɗaukaka ƙara zuwa gaban kotun koli.

APC ta fara sayar da fom na takara a zaben Edo

A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC mai mulki ta fara sayar da fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara ga mambobinta masu nufin neman gwamnan Edo.

Tsohon ƙaramin minista kasafi da tsare-tsaren kasa, Mista Clem Agba, shi ne ɗan takara na farko da ya lale N50m ya siya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel