Wata Sabuwa: Na Hannun Damar Wike Ya Yi Murabus Daga Matsayin Shugaban Ma’aikatan Fubara
- Shugaban maika'atan Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas, Chidi Amadi ya sauka daga kan kujerarsa
- Amadi wanda ya kasance mai biyayya ga ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi murabus daga kujerarsa ne a daidai lokacin da rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar ya ki ci ya ki cinyewa
- Da yake tabbatar da ci gaban, kwamishinan labarai da sadarwa na jihar Ribas, Joseph Johnson, ya ce Gwamna Fubara zai sanar da madadinsa a lokacin da ya kamata
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Port Harcourt, Jihar Rivers - Chidi Amadi, Shugaban maika'atan Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas, ya yi murabus daga kan kujerarsa.
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto a safiyar Alhamis, 11 ga watan Janairu, kwamishinan labarai da sadarwa na jihar Ribas, Joseph Johnson, ya tabbatar da murabus din Amadi.
Rikicin Ribas: Chidi Amadi ya yi murabus
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka shafe tsawon watanni ana rikicin siyasa a jihar da jam'iyyar PDP ke iko a cikinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Johnson ya ce Gwamna Fubara zai sanar da wanda zai maye gurbin Amadi, wanda ya kasance mai biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, a lokacin da ya dace.
Ya ce:
"Tsohon shugaban ma'aikata, Honb Chidi Amadi, ya yi murabus. Gwamnan zai sanar da sabon shugaban ma'aikata a lokacin da ya dace.
“Hakkin gwamna ne ya nada mukami a lokacin da ya so. Zai gaya mana kuma za mu sanar da ku kuma za ku sami sanarwa a kan haka."
Wike ya aika sakon gargadi ga Fubara
A baya mun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya tura sakon gargadi ga Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers. Wike ya bayyana cewa a yanzu ba lokacin siyasa ba ne amma idan lokacin ya yi za a gane waye ne a sama.
Ministan Abuja Wike ya yi kicibis da abokin karatunsa na sakanbdare, ya yi masa kyautar kudi a bidiyo
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Asabar 6 ga watan Disamba yayin ganawa da tsohon amininsa a siyasa, Cif Victor Giadom.
Ya ce bai damu da dukkan zage-zagen da ake yi a kafofin yada labarai ba inda ya ce ba a zabe a kafar sadarwa, cewar Vanguard.
Asali: Legit.ng