Kano: Kotun Koli Ta Tsayar Da Ranar Yanke Hukunci Kan Shari'ar Abba Da Gawuna
- Kotun Koli ta tsayar da ranar Juma'a 12 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Kano da aka dade ana jira
- Kotun Kolin ta ce hukuncinta zai nuna ko wanene halastaccen wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris na 2023 da aka yi a Jihar Kano
- Hukuncin babban kotun na kasa zai nuna makomar gwamnan Kano Yusuf, wanda a baya Kotun Daukaka Kara ta soke zabensa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Kotun Koli ta tsayar da ranar Juma'a 12 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan daukaka kara game da zaben gwamnan Kano.
Sakataren tawagar lauyoyin Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Barrister Bashir Tudun Wuzirci, ya tabbatar da hakan kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Eh, an tabbatar a hukumance. Sun fada mana mu taho kotu ranar Juma'a domin yanke hukunci. "Sun ce dukkan bangarorin kada su taho da lauyoyi fiye da biyu.
"Sun ce hakan ne domin za su yanke hukunci guda bakwai a ranar Juma'an," in ji shi.
Hakan na zuwa ne bayan Gwamnan na Kano Abba Kabir Yusuf wanda dade yana gwagwarmaya ya daukaka kara kan hukuncin Kotun Daukaka Kara, wacce ta tabbatar da soke zabensa.
Karamar kotun ta ayyana cewa dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Nasir Gawuna a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a ranar 18 ga watan Maris na 2023.
A dai ranar Juma'an ne za a kawo karshen faffatawa a kotu da ake dade ana yi tsakanin Gwamna Yusf na NNPP da Nasir Gawuna na APC.
Nesa ta zo kusa: Kotun koli ta sanya ranar yanke hukuncin kan zaben gwamnan Kano, Bauchi da wasu jihohi 5
Jam'iyyar APC tana da kwarin gwiwar ita za ta lashe zabe a Kotun Koli, ta raba wa mambobinta anko
A wani mataki da ke nuna kwarin gwiwa, jam'iyyar APC a jihar Kano ta rabawa mambobinta yadi na anko mai dauke da tambarin da ke hular Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ana yi wa lamarin kalon wani mataki ne da ke nuna yan jam'iyyar suna da yakinin sune za su yi nasara a zaben gwamnan na Kano.
A bangare guda, jam'iyyar ta NNPP ta mayar da lamari zuwa ga Allah, inda ta rika shirya addu'o'i domin nasarar Abba Kabir Yusuf a babban kotun na kasa.
Kano: NNPP Ta Sanar da Matsayarta Kan Hukuncin Kotun Koli Tare Da Matakin Na Gaba
Jam’iyyar NNPP ta bayyana rashin jin dadinta game da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, na korar gwamnan Kano, Abba Yusuf.
Jam'iyyar ta ce za ta binciki duk wata hanya ta doka da za ta kwato mata hakkinta.
Asali: Legit.ng