Ana Dab da Yanke Hukunci Shekarau Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Gawuna da Gwamna Abba

Ana Dab da Yanke Hukunci Shekarau Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Gawuna da Gwamna Abba

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi muhimmin kira ga jam'iyyun NNPP da APC a Kano
  • Tsohon sanatan ya buƙaci ɓnagarorin biyu da su amince da hukuncin da kotun ƙoli za ta yanke kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar da zuciya ɗaya
  • Shekarau ya shawarce su da su guji yon kalaman ƙiyayya ga juna domin hakan ba sanya su samu mulki ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, ya roƙi jam'iyyun NNPP da APC da su amince da hukuncin da kotun ƙoli za ta yanke da zuciya ɗaya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Shekarau ya yi wannan kiran ne a wata hira da gidan talabijin na Channels tv a shirin su na 'Siyasa a Yau'.

Kara karanta wannan

Kotun koli: Ana dab da yanke hukunci dan takarar gwamnan APC ya mika sabuwar bukata

Shekarau ya shawarci Abba da Gawuna
Shekarau ya bukaci yan bangarorin biyu da amince da hukuncin kotin koli da zuciya daya Hoto: Nasiru Yusuf Gawuna, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara dai sun kori Gwamna Abba Yusuf, kuma a halin yanzu gwamnan yana ƙalubalantar korarsa a gaban kotun ƙoli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan na Kano ya yi nuni da cewa ɗabi'ar siyasa ba da gaba ita ce ginshiƙin siyasarsa inda yake kallon abokanan siyarsa a matsayin abokansa ba tare da la'akari da bambancin da ke tsakaninsu ba.

Wane kira Shekarau ya yi wa NNPP da APC?

A kalamansa:

"Idan lokacin takara ya yi sai mu shiga fage kuma da zarar an gudanar da zaɓe kuma aka bayyana wanda ya yi nasara, halina shi ne, idan kana da wata hujja ƙarara ta rashin gaskiya za ka iya kai ƙara.
"Kuma da zarar kotu ta yanke hukuncinta, kuma an je har zuwa matakin ƙarshe, da zarar an yi haka wasan ya ƙare, sai mu yi shirin tunkarar zaɓe na gaba.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya bayyana dalilin da ya sa ba za a kira gwamnatin Buhari matsayin wacce ta gaza ba

"Yanzu haka suna kotu kan zaɓen gwamnan Kano, muna nan mun zura ido. Ina ba jam’iyyun NNPP da APC shawara cewa da zarar kotun ƙoli ta yanke hukunci, a amince a zauna.
"Kuma ina kira gare su cewa cin zarafi, ƙiyayya da kalaman ƙiyayya ba za su bayar ko hana mulki ba.”

APC Ta Hango Nasara a Kotun Ƙoli

Rahoto ya zo cewa jam'iyyar APC a jihar Kano ta hango yin nasara kan jam'iyyar NNPP a kotun ƙoli kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano.

Magoya bayan jam'iyyar tuni suka fara rabon kayan ankon da za su sanya a ramar rantsar da Nasiru Yusuf Gawuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng