Gwamnan APC Ya Kori Dukkan Kwamishinoni da Hadiman Gwamnatinsa a Arewa, Ya Faɗi Dalili
- Gwamna mai barin gado, Yahaya Bello, ya sallami dukkan mambobin majalisar zartarwan jihar Kogi banda kaɗan kada ciki
- Bello ya ɗauki wannan matakin ne yayin da wa'adin mulkinsa na zango biyu ke dab da ƙarewa bayan zaɓen gwamna a watan Nuwamba
- Sakataren watsa labaran gwamnan ya umarci dukkan waɗanda aka kora sun miƙa mulki da kayayyakin gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya rusa majalisar zartaswa ta jihar tare da korar shugabannin wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnati.
Wannan mataki da gwamnan ya ɗauka ya zo ne a daidai lokacin da wa'adin mulkinsa na tsawon shekaru takwas ke dab da karewa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan Kogi, Mohammed Onogwu, ya fitar a Lokoja, babban birnin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda aka sauke daga mukaminsu sun hada da shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Jamiu Asuku, da Akanta Janar na jihar, Alhaji Jibrin Momoh da dai sauransu.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwar jihar a fadar gwamnati dake Lokoja.
Gwamnan Bello ya yabawa waɗanda matakin ya shafa bisa nuna kwazo da kishin kasa maras misaltuwa a duk lokacin da suke yi wa jihar hidima.
Sanarwan ta ce:
"Ana umurtan waɗanda abin ya shafa su mika mulki, tare da mika duk wasu takardu, kadarori, da kayan gwamnati ga babban sakatare na ma’aikatun su ko kuma manyan jami’an gwamnati da ke zaune a ofisoshinsu."
Waɗanda gwamnan bai kora daga aiki ba
Sakataren yaɗa labaran gwamnan ya ƙara da cewa Bello ya riƙe wasu kwamishinoni, shugabannin hukumomi da hadimai, matakin korar bai shafe su ba.
Waɗanda Gwamna Bello ya umarci su ci gaba da zama kan muƙamansu sun haɗa da sakataren gwamnatin jiha, Ayoade Folashade Arike da mai bada shawara kan tsaro, Rtd Navy Commodore Jerry Omodara.
Sauran sune kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa, Kinsley Fanwo da takwarorinsa na ma'aikatun ilimi, kuɗi, kananan hukumomi da sauransu.
Kotu ta raba gardama kan kujerar sakataren PDP
A wani rahoton kuma Babbar kotun birnin Abuja ta yanke hukunci kan taƙaddamar kujerar sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa.
Yayin yanke hukunci ranar Talata, kotun ta tabbatar da Sanata Samuel Anayanwu a matsayin sakataren PDP.
Asali: Legit.ng