Betta Edu: Tinubu Ya Dakatar Da Minista 1 Daga Aiki Nan Take, Ya Bai Wa EFCC Sabon Umarni

Betta Edu: Tinubu Ya Dakatar Da Minista 1 Daga Aiki Nan Take, Ya Bai Wa EFCC Sabon Umarni

  • Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Dokta Betta Edu daga matsayin ministar harkokin jin kai da yaƙi da talauci kan badaƙalar kuɗi
  • Shugaban ƙasar ya kuma umarci hukumar EFCC ta gudanar da bincike kan zargiin da ake wa ministar da wata hukuma
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan mai magana da yawun Edu ya yi karin haske kan kuɗin da aka tura wani asusu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaba Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da ministar harkokin jin kai da yaki da talauci, Dokta Betta Edu daga aiki ba tare da bata lokaci ba.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, shi ne ya bayyana dakatar da ministar a wata sanarwa da aka wallafa a shafin fadar shugaban ƙasa na X ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kori wasu manyan mutane 2 da Buhari ya naɗa, ya faɗi muhimmin dalili

Shugaba Tinubu da Betta Edu.
Shugaba Tinubu Ya Dakatar da Ministar Harkokin Jin Kai da Yaye Talauci, Betta Edu Hoto: Bayo Onanuga, Betta Edu
Asali: Facebook

Shugaba Tinubu ya ce dakatarwar wani ɓangare ne na alwashin da ya ɗauka na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkomin tafiyar da mulkin al’ummar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma umarci shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ya gudanar da bincike mai zurfi kan badaƙalar da ake zargin da hannun ma'aikatar jin ƙai.

Sanarwan ta ci gaba da cewa:

"Ana umurtan Ministar da aka dakatar da ta mika harkokin mulki ga babban sakataren ma’aikatar jin kai da yaki da fatara ta tarayya kuma ta bada haɗin kai a binciken da za a yi."

Me ya jawo aka dakatar da Betta Edu?

Wata wasiƙa da ta bayyana mai ɗauke da sa hannun Dokta Edu da adireshin Akanta Janar ta ƙasa ta nuna cewa dakatacciyar ministar ta bada umarnin tura wasu kudi a asusun kai da kai na Bridget Mojisola Oniyelu.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin masu mukamin da Tinubu ya nada kuma ya dakatar/cire su kasa da shekara 1

Takardar wacce ta yaɗu ta nuna cewa an tura kuɗin daga baitul mali zuwa asusun kai da kai na Oniyelu da yawun Betta Edu.

Mai taimaka wa ministar kan harkokin yada labarai, Rasheed Zubair, a cikin wata sanarwa daya fitar ranar Juma’a ya ce tura kuɗin ya cika dukkan sharuɗɗan da doka ta tanada.

Jerin kararrakin da kotun koli zata saurara a mako 1

A wani rahoton na daban A wannan makon kotun koli za ta saurari kararraki 21 da suka taso daga takaddamar zaben gwamna da aka yi.ranar 18 ga Maris, 2023.

Mun tattara muku dukkan kararrakin da za a tattake wuri a kansu a kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya da waɗanda mai yiwuwa za a yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262