Kotun Koli: Ana Dab da Yanke Hukunci Dan Takarar Gwamnan APC Ya Mika Sabuwar Bukata

Kotun Koli: Ana Dab da Yanke Hukunci Dan Takarar Gwamnan APC Ya Mika Sabuwar Bukata

  • Ɗan takarar gwamnan APC a jihar Plateau, Nentawe Yilwatda, ya buƙaci kotun ƙoli da ta yi watsi da buƙatar Gwamna Caleb Mutfwang
  • Nentawe ya buƙaci kotun da ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka wanda ya ba shi nasara a zaɓen gwamnan jihar
  • Gwamna Mutfwang ya garzaya kotun ne dai yana neman kotun ƙolin da ta soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na soke zaɓensa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Ɗan takarar gwamnan jihar Plateau a jam’iyyar APC, Nentawe Yilwatda, ya buƙaci kotun ƙoli ta yi watsi da ƙarar da Gwamna Caleb Mutfwang ya shigar gabanta.

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnan na jam'iyyar PDP dai ya yi zargin kotun ɗaukaka ƙara ba ta yi masa adalci ba, bayan ta soke zaɓensa tare da ba Nentawe nasara.

Kara karanta wannan

Kotun koli ta raba gardama a shari'ar zaben gwamnan APC a jihar Arewa

Nentawe ya aike da sabuwar bukata gaban kotun koli
Kotun koli na dab da yanke kan shari'ar zaben gwamnan jihar Plateau Hoto: Caleb Mutfwang, Nentawe Yilwatda
Asali: Twitter

Kotun dai ta kori Gwamna Mutfwang ne bisa dalilin cewa jam’iyyarsa ta PDP ba ta da tsarin ɗaukar nauyin ɗan takara a zaɓe, inda daga bisani ta bayyana Yilwatda a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Mutfwang a cikin bayanin da ya yi a kotun ƙoli ya tabo batutuwan da suka shafi rashin adalci a sauraron ƙarar da kotun ɗaukaka ƙara ta yi na tsige shi a matsayin gwamnan jihar.

Wacce buƙata Nentawe ya nema?

Sai dai Yilwatda, ta bakin lauyansa, Farfesa Kayode Olatoke, a martanin da ya mayar kan dalilan ɗaukaka ƙara da Mutfwang ya shigar a gaban kotun ƙoli, ya ce kotun ɗaukaka ƙara ta yi wa dukkanin ɓangarorin adalci kuma ta yi daidai da ta kori gwamnan.

Ya yi nuni da cewa abin da suke jayayya akai shi ne "cancanta/ɗaukar nauyi" na Gwamna Mutfwang, inda ya buƙaci kotun ƙolin da ta tabbatar cewa PDP ba ta da ikon ɗaukar nauyin wani ɗan takara a zaɓen 2023, rahoton Blueprint ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana gwamnoni, sanatoci da yan majalisar da za su dawo APC

Ɗan takarar na APC ya kuma shaida wa kotun ƙolin cewa akwai wasu hukunce-hukunce da suka yanke cewa batun cancantar ɗan takara abu ne na gabanin zaɓe da kuma bayan zaɓe.

Don haka ya buƙaci kotun koli da ta yi watsi da ƙarar tare da tabbatar da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke.

Malamin Addini Ya Bayyana Makomar Gwamna Mutfwang

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen malamin addinin Kirista, Fasto Joshua Iginla, ya yi hasashen makomar Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau a kotun ƙoli.

Malamin addinin ya bayyana cewa dole sai gwamnan ya dage da addu'a domin ya hango babbar matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng