Shugaban APC Ya Ambaci Mutum 1 da Ake Rokon Allah Ya Sauya Sheka Daga PDP
- Babban jigo a jam’iyyar APC, Victor Giadom ya ce ana addu’a Nyesom Wike ya sauya sheka daga PDP
- Shugabannin APC mai mulki a Najeriya suna rokon Allah Ministan harkokin Abuja ya canza shawara
- Cif Giadom ya ji dadin yadda Nyesom Wike ya taimakawa takarar Bola Tinubu a Ribas a zaben 2023
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Rivers - Shugaban APC a Kudu maso kudancin Najeriya, Victor Giadom, ya yi kira ga Nyesom Wike ya canza sheka daga PDP.
Mataimakin shugaban na jam’iyyar APC na kasa, Cif Victor Giadom yana zawarcin Ministan harkokin Abuja, Punch ta fitar da labarin.
Victor Giadom ya yi wannan kira ne a yayin da ya karbi ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas da su ka fice daga PDP zuwa APC mai-ci.
Akwai kitimutmura a 2027: Tawagar G5 ta PDP a ta marawa shugaba Tinubu baya a zaben 2027, Inji Ortom
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan siyasar ya gabatar da jawabi da ake taron murnar shiga sabuwar shekara wanda Nyesom Wike ya shiya a garin Rumueprikom.
Nyesom Wike zai bar PDP zuwa APC?
Kafar Ministan harkokin Abujan daya ta bar PDP, ana tunani ya jefa guda a jam’iyyar APC tun da ya fadi zaben tsaida gwani a 2022.
Giadom ya ce ana ta faman tattaunawa da yin adduo’i domin ganin tsohon gwamnan na jihar Ribas ya sake tunani, ya fice daga PDP.
Giadom: Wike ya taimakawa APC a 2023
A jawabin da ya yi a karamar hukumar Obio/Akpor, jagoran na APC ya godewa Wike a kan irin gudumuwar da ya ba Bola Tinubu.
An rahoto Giadom yana cewa tsohon gwamnan ya taimaki APC a zaben shugaban kasa a 2023 kamar yadda ake zargin ‘dan siyasar.
"Mun tuntubi masu addu’o’i da yawa domin ka canza shawara kuma ka bar PDP ka shigo jam’iyyarmu (APC).
Na tabbata wannan addu’ar za tayi aiki."
- Victor Giadom
Daga baya Giadom ya gayyaci Wike zuwa mahaifarsa ta Bera a karamar hukumar Gokana, a nan ya ce ya ji dadi da APC ta karbe majalisa.
'Dan siyasar ya ce sai zuwa zaben 2027 za a gane nauyin kowane 'dan siyasa a Ribas.
Shari'ar zaben 2023
A wani rahoton dabam, an ji Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna sun kusa sanin makomarsu bayan watanni ana shari’a a kotuna.
Kotun koli za ta yi hukunci tsakanin jam’iyyun APC, PDP da LP a kan nasarar Babajide Sanwo Olu wanda ya lashe zaben tazarce.
Asali: Legit.ng