Rikicin APC: Kotu ta haramtawa Victor Giadom alakanta kansa da jam'iyyar APC

Rikicin APC: Kotu ta haramtawa Victor Giadom alakanta kansa da jam'iyyar APC

Wata kotun jihar Ribas ta haramtawa mataimakin sakataren uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Victor Giadom ikirarin kansa da kasancewa mamban APC ko shugabanta.

The Nation ta samu rahoton cewa Alkali C. Nwogu ya bada umurnin haka ne a karar da Okechukwu Chidor Ogbonna da Mac-Lords Peterson suka shigar kan jam'iyyar APC na yankin Rivers, mukaddashin jam'iyyar na Rivers Igo Aguma; Victor Giadom da Golden Chioma.

Kotun ta ce tun da kwamitin zartarwar jam'iyyar APC na jihar ta dakatad da Victor Giadom, kada ya sake alakanta kansa da jam'iyyar ko ayyukanta har sai an kammala shari'ar.

Alkalin yace: "An bada umurnin haramtawa mai amsa zargi na uku daga ikirarin kansa matsayin mamba ko jami'in jam'iyyar....ko yin wani abu da ya halasta ga mambobi."

Alkalin ya dage karar zuwa ranar 9 ga Yuli, 2020 domin cigaba da sauraron kara.

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnan Ondo ya sallami dukkan hadiman mataimakinsa

Rikicin APC: Kotu ta haramtawa Victor Giadom alakanta kansa da jam'iyyar APC
Rikicin APC: Kotu ta haramtawa Victor Giadom
Asali: UGC

Da safiyar yau Laraba, Wasu jami'an yan sanda sun kulle hedkwatar uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) bisa umurnin Sifeto Janar na hukumar yan sanda, IGP Mohammed Adamu.

An samu labarin cewa IGP na yan sanda zai gana da bangarorin kwamitin gudanarwan jam'iyyar a hedkwatar hukumar misalin karfe 1 na rana.

An tattaro cewa kwamishanan yan sandan birnin tarayya ne ya umurci babban jami'in tsaron hedkwatar ya bayyanawa mambobin kwamitin gudanarwan jam'iyyar cewa babu wanda aka amince ya shiga harabar hedkwatar.

Rikicin jam'iyyar APC ya dau sabon salo ne bayan hukuncin kotun daukaka kara da ya tabbatar da dakatad da Adams Oshiomole matsayin shugaban uwar jam'iyyar.

Tun daga lokacin kwamitin gudanarwan jam'iyyar ta nada tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, a matsayin shugaban kungiyar na riko, amma mataimakin sakataren jam'iyyar, Victor Giadom ya ce sam shine sahihin shugaban jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

iiq_pixel