Rikici Ya Barke a APC Bayan Dan Tsohon Sifetan Yan Sanda Ya Samu Damar Gadon Kujerar Ministan Tinubu

Rikici Ya Barke a APC Bayan Dan Tsohon Sifetan Yan Sanda Ya Samu Damar Gadon Kujerar Ministan Tinubu

  • Dan tsohon Sifetan 'yan sandan Nigeria, Sunday Ehindero ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani a jihar Ondo
  • Ifeoluwa Ehindero ya yi nasarar a zaben da aka gudanar da ke cike da rikici wanda aka yi ta zanga-zanga
  • Hakan ya biyo bayan ayyana kujerar a matasyin babu mai ita bayan Olabunji Tunji-Ojo ya karbi mukamin Ministan Cikin Gida

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo – An samu hatsaniya yayin gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Ondo a kokarin maye gurbin Ministan Tinubu da ya bar kujerar.

Akalla ‘yan takara guda takwas ne suka fito neman kujerar a mazabar Akoko a Majalisar Tarayya.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Ministar da Tinubu ta dakatar

An sake samun barkewar rikici bayan zaben fidda gwani a APC
Tsohon dan Sifetan 'yan sanda ya lashe zaben fidda gwani a Ondo. Hoto: @ImamShams.
Asali: Twitter

Su waye ke kalubalantar zaben fidda gwanin a Ondo?

The Nation ta tattaro cewa an ayyana kujerar a matasyin babu mai ita bayan Olabunji Tunji-Ojo ya karbi mukamin Ministan Cikin Gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin masu neman kujerar sun hada da Olugbenga Araoyinbo da Olarewaju Kazeem da Lasisi Planipekun.

Sauran sun hada da Haruna Adesina da Charles Babalola da kuma dan tsohon Sifetan rundunar ‘yan sanda, Ifeoluwa Ehindero.

Ifeoluwa Ehindero shi ne ya yi nasarar lashe zaben a matsayin wanda zai yi takara a zaben da za a gudanar a watan Faburairu.

Mene dalilin zanga-zangar a Ondo?

An jibge jami’an tsaro a harabar da aka gudanar da zaben fidda gwanin yayin da ake zanga-zangar kin amincewa da wanda ya yi nasara.

Sun bayyana rashin gamsuwarsu bayan an sauya sunayen wadanda suka sani da nufin za su yi zaben tun a unguwanni.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe basarake da wani manomi, sun tafka mummunar ɓarna a jihohin arewa 2

Tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar jihar, Olugbenga Araoyinbo shi ya ankarar da sauran ‘yan takarar kan irin magudin da aka shirya.

Ya ce dokar zaben ba ta ba da damar mutum daya ya zauna ya zabi sunayen wadanda za su yi zaben shi kadai ba, cewar Daily Trust.

APC ta bayyana mai gadar kujerar Ministan Tinubu

A wani labarin, Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta zabi wanda zai maye gurbin kujerar Sanata Dave Umahi a jihar Ebonyi.

Farfesa Anthony Okorie Ani shi ya yi nasarar lashe zaben da aka gudanar wanda za a yi a farkon watan Faburairu mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.