Tsohon Ministan Buhari Ya Tsoma Baki, Ya Fallasa Shirin APC Na Kwace Mulki Daga Gwamna Mai Ci
- Tsohon ministan kwadago a mulkin Muhammadu Buhari ya ce APC ta shirya karɓe mulkin jihar Anambra a zaben 2025
- Dakta Chris Ngige ya bayyana cewa ya san APC ta rabu gida biyu a Anambra amma zasu ɗinke ɓarakar gabanin zaben
- Ngige ya faɗi haka ne a wurin wani taro da aka shirya a gidansa wanda aka rabawa masu ƙaramin karfi kayan tallafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Anambra - Tsohon ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige, ya bayyana shirin jam'iyyar APC na karɓe mulkin wasu jihohi a zaɓe na gaba.
Ngige ya ce All Progressives Congress (APC) ta shirya kwace mulki daga hannun jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a jihar Anambra a shekarar 2025.
Ngige, tsohon gwamnan jihar Anambra ya yi wannan furucin ne ranar Asabar a yayin wani taro a gidansa da ke Alor, ƙaramar hukumar Idemili ta Kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shirya taron ne domin rabawa mambobin jam’iyyar APC, nakasassu, da kuma tsofaffi tallafin kayan abinci, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Zamu warware saɓanin cikin gida - Ngige
Duk da ya amince cewa jam’iyyar APC ta dare gida biyua jihar, Ngige ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta yi nasara a zaben gwamna na 2025.
Tsohon ministan ya tabbatar da cewa za a warware saɓanin da ya shiga tsakanin mambobin jam'iyyar gabanin zaben gwamnan Anambra mai zuwa.
A kalamansa ya ce:
"Hakika muna da bangarori biyu a jam’iyyar APC ta jiha, ba zan musanta hakan ba. Ni duka uba ne ga kowane tsagi kuma abin duba da koyi a APC reshen Anambra.
"Ina sane da cewa an samu sabbin mambobin da suka haɗe da mu tun 2021. Jam’iyyar kamar coci ce; tana maraba da sabbin masu neman ceto ko kuma goyon bayan gwamnati mai ci."
Ya jaddada cewa domin samun nasara dole a yi aiki tuƙiru, inda ya kuma yi gargadi game da yin magudin zabe, yana mai cewa irin wadannan ayyuka sun zama tsohon yayi.
Ngige ya ƙara da cewa a halin yanzu yana hutawa ne, amma a watan Mayun 2025, zai yanke shawara kan matakin da zai dauka na gaba a siyasa, The Nation ta ruwaito.
NNPCL da yan kasuwa sun cimma matsaya
A wani rahoton kuma kamfanin mai na kasa NNPC da ƴan kasuwar mai sun kawo karshen raɗe-raɗin kara farashin litar man fetur a Najeriya.
Ƴan kasuwa sun nuna cikakken goyon bayansu ga matakin NNPC na barin litar mai a kan N600 da N630 ba tare an samu ƙari ba.
Asali: Legit.ng