Ku Sake Ba Ni Dama: Tsohon Gwamnan Arewa Ya Fadi Darussan Da Ya Koya a Gidan Kaso, Ya Tura Bukata
- Jolly Nyame, Tsohon gwamnan jihar Taraba ya bayyana abubuwan da ya koya yayin zaman kaso a gidan yarin Kuje
- Nyame ya bayyana cewa a yanzu zai shugabanci jihar yadda ya kamata inda ya ce ya karu da wasu hikimomi a gidan kason
- Nyame ya bayyana haka a wani taro a sakatariyar kungiyar CAN a Jalingo a yau Juma'a 5 ga watan Janairu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Taraba - Tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame ya bayyana darussan da ya koya yayin zaman gidan yari.
Tsohon gwamnan ya ce idan za a bashi dama ta biyu zai kasance nagartaccen shugaba saboda abubuwan da ya koya.
Mene Nyame ke cewa kan sake ba shi dama?
Nyame ya bayyana haka a wani taro a sakatariyar kungiyar CAN a Jalingo a yau Juma'a 5 ga watan Janairu, kamar yadda Vanguard ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jolly ya ce tabbas zamansa a gidan yarin Kuje da ke birnin Tarayya Abuja ya koya masa abubuwa da dama masu amfani.
Ya ce darussan sun sake gyara shi a matsayin shugaba nagari idan zai sake samun damar mulkar jihar, cewar Daily Post.
Wace shawara Nyame ya bai wa 'yan Najeriya?
A cewarsa:
"Na koyi abubuwa da dama a gidan kason Kuje da kuma cikin asibiti.
"Idan na sake samun damar mulkar mutanen jihar Taraba tabbas zan yi ingantaccen mulki saboda abin da na koya."
Ya shawarci 'yan Najeriya kan addu'o'i don samun zaman lafiya a kasar da kuma hadin kai.
Nyame wanda ya yi shekaru hudu kacal daga 14 da aka yanke masa inda ya zargi 'yan siyasa da masa bita-da-kulli.
Gwamna Caleb ya roki Kotun Koli ta yi masa adalci
A wani labarin, Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya zargi Kotun Daukaka Kara da rashin yi masa adalci a shari'ar zaben jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa ba a ba shi damar bayani ba game da hujjoji takwas da ya gabatar a kotun.
Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin shari'ar zaben gwamnan jihar a farkon wannan shekara.
Asali: Legit.ng