Gwamnan APC Ya Rantsar da Sabbin Ciyamomi 38 da Mataimakansu, Sun Kama Aiki Gadan-Gadan
- Sabbin shugabannin kananan hukumomi 38 da mataimakansu sun karɓi rantsuwar kama aiki ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu
- Gwamna Biodun Oyebanji ya ja kunnen ciyamomin kan sha'anin tsaro, inda ya gaya musu ba zai lamurci gazawa ba
- A watan Disamban shekarar da ta gabata, 2023 aka yi zaben kananan hukumomi da kansiloli a jihar Ekiti
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ekiti - Gwamnan jihar Ekiti, Dakta Biodun Oyebanji, ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi 38 da mataimakan su ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu, 2024.
Da yake jawabi a wurin bikin rantsuwar kama aikin ciyamomin, Gwamna Oyebanji ya bukaci su maida hankali wajen kawo ci gaba da samar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
Ya kuma nemi sabbin ciyamomin su yi amfani da basirarsu wajen lalubo wasu hanyoyin samun kuɗin shiga da zasu taimaka wajen zuba ayyukan raya ƙasa, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oyebanji ya bada umarnin nan take ga ciyamomin domin su sake farfado da ayyukan ci gaba ta hanyar ɗorawa daga kakkarfan ginshikin da magabatan su suka shimfida.
Ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta amince da duk wani nau'i na tabarbarewar tsaro a matakin gwamnati na uku wanda ke karkashin ciyamomin ba.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne a Ado-Ekiti yayin bikin rantsar da sabbin ciyamomi wanda ya gudana a Osuntokun Pavillion, gidan gwamnati, Ado Ekiti.
An zabi sabbin shugabannin ne a lokacin zaben kananan hukumomin jihar Ekiti wanda aka yi a ranar 2 ga Disamba, 2023, kamar yadda Daily Post ta tattaro.
Ba zan yarda da gazawa a bangaren tsaro ba - Oyebanji
Da yake tsokaci kan aniyarsa ta kakkaɓe 'yan bindiga, masu garkuwa da sauran 'yan ta'adda a Ekiti, Gwamnan ya buƙaci ciyamomin su bada fifiko kan batun tsaro.
Oyebanji, wanda mataimakinsa, Monisade Afuye, ya wakilta ya ce:
“Ya kamata ku gaggauta kawo mun tsare-tsaren tsaro da dabarun ku ta ofishin mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro, da zarar kun karbi ragamar mulki."
"Ba zan yarda da gazawa a sha'anin tsaro ba, saboda haka, ku tabbatar da cewa kun jawo duk masu ruwa da tsaki kuna aiki tare."
Shugaba Tinubu ya yi naɗe-naɗe
A wani rahoton kun san cewa Bayan sallamar manyan daraktoci a hukumomin NPA da NIMASA, Shugaba Tinubu ya nada sabbin jini
Tinubu ya sanar da nadin nasu ne a yau Alhamis 4 ga watan Janairu ta bakin hadiminsa, Ajuri Ngelale.
Asali: Legit.ng