Babban Malamin Addini Ya Yi Hasashen Matsala Ga PDP, Ya Bayyana Babban Gwamnanta da Zai Koma APC
- Primate Babatunde Elijah Ayodele na cocin INRI Spiritual Evangelical ya yi hasashen ficewar Umo Bassey Eno daga jam’iyyar PDP
- Umo Bassey Eno shine gwamnan jihar Akwa Ibom a yanzu, jihar dake a shiyyar Kudu maso Kudu mai arziƙin man fetur
- Primate Ayodele ya yi hasashen cewa gwamnan na jihar Akwa Ibom zai koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Uyo, jihar Akwa Ibom - Primate Babatunde Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa nan ba da jimawa ba Fasto Umo Eno, gwamnan jihar Akwa Ibom, zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Gwamna Eno jigo ne a jam’iyyar PDP, jam’iyyar da ta kai shi ga samun nasara a zaɓen 2023 da ya gabata.
Da yake bayyana hasashen nasa ta shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), Ayodele, wanda ya kafa cocin INRI Evangelical Spiritual, ya tabbatar da cewa "PDP za ta yi asarar Akwa Ibom".
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ku fara yin cikakken gyara - Ayodele ga PDP
Babban malamin addinin ya kuma shawarci babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya da ta zaɓi kawo gyare-gyare a tsarinta.
A kalamansa:
“PDP za ta yi asarar Akwa Ibom. Da alamu Gwamna Eno zai wuce APC nan bada jimawa ba.
"PDP, dole ne ku koma ku daidaita wasu abubuwa a tambarin ku, kuna buƙatar sake fasalin tambarin, kuma ku sauya takenku.
"Idan ba ku sauya taken ku ba, babu abin da zai yi muku daidai a 2027."
Ayodele ya hasaso yadda PDP za ta ƙwace mulki a hannun APC
Primate Ayodele ya yi sabon hasashen kan yadda jam'iyyar PDP za ta ƙwace ragamar mulkin ƙasar nan a hannun jam'iyyar APC
Babban faston ya bayyana cewa jam'iyyar PDP za ta dawo kan madafun iko ne kawai idan ta magance rikicin cikin gida da take fama da shi.
Ayodele Ya Yi Hasashe Kan Alaƙar Tinubu, Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa Primate Ayodele ya yi hasashe kan yadda dangantakar Shugaba Tinubu da Wike za ta kaya.
Babban faston ya yi hasashen cewa za a samu matsala ta siyasa tsakanin Wike da Tinubu, wacce za ta kai ga ɓarkewar rikici a tsakaninsu.
Asali: Legit.ng