Tsohon Gwamna Ya Fadi Hakikanin Halin da Buhari Ya Damkawa Tinubu Asusun Najeriya
- Cif Olusegun Osoba ya ce da aka canza gwamnatin tarayya, sai aka samu baitul-mali babu komai a cikinsa
- ‘Dan siyasar ya ce ya zama dole Bola Ahmed Tinubu ya ci bashin kudi akalla har zuwa bayan shekara guda
- A lokacin da Muhammadu Buhari ya bar Aso Rock, wasu suna zargin an yi kaca-kaca da tattalin arzikin kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ogun - Dattijo kuma tsohon gwamna a jihar Ogun, Olusegun Osoba ya ce babu abin da Bola Ahmed Tinubu ya samu cikin baitul-mali.
A wata hira da aka yi da shi a tashar Arise a makon nan, Cif Olusegun Osoba ya tofa albarkacin bakinsa kan irin halin da ake ciki.
Tun kafin Muhammadu Buhari ya bar ofis a Mayun 2023, ‘dan siyasar ya ce ana cikin kalubale ta fuskar tattalin arziki a Najeriya.
Bola Tinubu zai kawo sauki a 2024?
Tsohon gwamnan ya ce Mai girma Bola Tinubu yana bakin kokarinsa wajen ganin ya kawar da wahalhalun da al’ummarsa ke sha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da aikin gama ya gama, This Day ta ce Segun Osoba ya ce sai da a sa ran abubuwa za su gyaru cikin 2024 da aka shiga.
Osoba ya ce dole Tinubu ya ci bashi
"An yi wa baitul-mali wayam, tsohuwar gwamnati tana cin bashi domin biyan albashi, kusan babu komai a ko ina.
Meya rage ayi a lokacin in ban da a ci bashi domin a cike gibin?
Hakan bai nufin a cigaba da al’adar cin bashi har abada. Bayan shekarar farko a ofis, za a sake dubawa a ga ya za ayi.
- Segun Osoba
Saura kiris abubuwa su ruguje a Najeriya
Na yi maku bayani cewa mun yi sa’a, amma zuwa 1 ga watan Yuni, an shirya komai zai ruguje gaba daya.
Ina fada maku idan ba don shi (Tinubu) ya dauki hanyar da gwamnati ta dauka ba, da komai ya ruguje.
- Segun Osoba
Laifin Muhammadu Buhari ne ko kuwa?
Da Punch ta yi hira da Adebayo Folorunsho Francis kwanaki, ya fadi irin hakan, ya ce Muhammadu Buhari ya bar baya da kura a kasar.
Tsohon shugaban na APC a Legas ya ce tun ba yau ba tattalin arziki ya ruguje, ya kuma ce haka abin yake har a wasu kasashen waje.
Tsare-tsaren da Tinubu ya kawo
Kun ji labari ana zargin Gwamnatin Bola Tinubu ta dawo da tallafi ta bayan-fage, domin ainihin farashin man fetur ya zarce N1, 000.
Masana da wasu ‘yan kasuwa sun karyata kamfanin NNPCL, sun ce farashin fetur ya fi karfin N2, 500 a kasashen waje a kasuwar yau.
Asali: Legit.ng