Hadimin Atiku Ya Yi Magana Kan Ko Dan Takarar Na PDP Sai Sake Tsayawa Takarar Shugaban Kasa

Hadimin Atiku Ya Yi Magana Kan Ko Dan Takarar Na PDP Sai Sake Tsayawa Takarar Shugaban Kasa

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

FCT Abuja - Daniel Bwala, tsohon mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ta Atiku Abubakar, ya ce jigon na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zai sake takarar kujerar shugaban kasa a 2027.

Bwala ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television a daren ranar Talata 2 ga watan Janairu.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar mai shekara 77 har yanzu yana fatar zama shugaban kasa. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku bai karaya da neman shugabancin kasa ba

Legit.ng ta rahoto cewa Atiku, dan shekara 77, ya yi takarar shugaban kasar Najeriya sau shida bai yi nasara ba, a 1993, 2007, 2011, 2015, 2019 da 2023.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa ya kamata Atiku ya hakura da takarar shugaban kasa, Deji Adeyanju

Da aka masa tambaya ko yana ganin tsohon mataimakin shugaban kasar zai sake takara, Daniel na PDP ya bada amsa kamar haka:

"Tabbas, zai sake takara. Ya cancanta, yana da hikima, yana da ilimi, yana da karfi da kuzari, kuma shine shugaban kasa wanda bamu samu ba, maganan gaskiya, idan akwai wani dan siyasa da ya fahimci yan kasuwa, Atiku Abubakar ne. Kuma wannan tattalin arzikin namu zai iya farfadowa ne kawai idan an bari yan kasuwa su ja ragamar ta."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164