Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Raba Motoci 60 a Jihar Kano, Ya Faɗi Muhimmin Dalili 1

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Raba Motoci 60 a Jihar Kano, Ya Faɗi Muhimmin Dalili 1

  • Sanata Barau Jibrin ya raba motocin Sharon guda 60 da mazauna jihar Kano domin taimaka masu su dogara da kansu
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce wannan ba shi ne na farko kuma ba zai zama na ƙarshe ba da izinin Allah
  • Ya kuma roƙi duk mutanen da suka ci gajiyar tallafin motar su dage wajen gina kansu da kuma waɗanda ke kewaye da su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau ya raba motocin Sharon guda 60 ga wasu mazauna jihar Kano.

Bikin rabon motocin ga waɗanda Allah ya tsaga da rabonsu ya samu halartan ɗumbin mutanen mazaɓarsa da magoya bayansa da kuma masu fatan alheri a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Allah Sarki: An samu asarar rayukan bayin Allah a wani mummunan hatsarin mota

Sanata Barau Jibrin.
Tallafi: Sanata Barau Jibrin Ya Raba Motoci 6 a Jihar Kano Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban majalisar, Ismail Mudashir, ya fitar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, wadanda suka ci gajiyar wannan tallafin sun fito daga dukkan sassan jihar, sun hada da ‘yan kasuwa, manoma, ma’aikatan gwamnati da ‘yan siyasa da dai sauransu.

Meyasa Barau ya raba motocin?

Da yake raba motocin, Sanata Barau ya ce an yi hakan ne domin a sassauta wa wadanda suka amfana wajen zuwa wuraren aiki, kasuwanci da gonakinsu da nufin bunkasa tattalin arzikin Kano.

Ta bakin shugaban ma’aikatansa, Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi, ya nanata kudurinsa na ganin al’ummar mazabar sun zama masu dogaro da kansu da kuma bayar da gudunmowa wajen habaka tattalin arzikin kasa.

Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar rabon motocin da su yi amfani da su wajen karfafawa da gina kansu da sauran al’ummar yankin.

Kara karanta wannan

Bayan ya samu babbar matsala, gwamnan PDP ya yi magana kan hakura da mukaminsa

Ya ce:

"A yau mun taru a nan domin rabon motoci 60 a wani bangare na kokarin da mataimakin shugaban majalisar dattawa ke yi na baiwa al’ummarmu damar dogaro da kai."
"Da wadannan motoci, mutanen da aka raba wa za su samu damar gudanar da sana’o’insu yadda ya kamata tare da bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban jihar."
"Wannan ba shi ne na farko ba kuma ba zai zama na ƙarshe ba da yardar Allah, zai ci gaba da aiwatar da irin waɗan nan tallafin na agaji don baiwa mutanenmu damar dogaro da kai."

Ɗan takarar gwamna a 2023 zai koma APC

A wani rahoton kuma Magnus Abe, ɗan takarar gwamnan jihar Ribas a inuwar SDP a zaben 2023 ya tabbatar da jam'iyyar da zai koma a yanzu.

Tsohon sanatan ya bayyana cewa ƴan majalisa 27 na majalisar dokokin jihar Ribas sun tsira a yanzu amma akwai wata matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262