Muhimmin Abu 1 Tak da Ya Sa Ya Kamata Shugaban Hukumar Zaɓe INEC Na Kasa Ya Yi Murabus
- Yadda babban zaɓen 2023 ya gudana kaɗai ya isa ya sa shugaban hukumar zabe ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, yin murabus
- Farfesa Jideofor Adibe na jami'ar jihar Nasarawa ne ya bayyana haka bisa wasu hujjoji da ya dogara da su
- Ya ce matuƙar ana son gyara a yanayin zaben Najeriya, tilas Yakubu ya haƙura da jagorancin INEC domin ya gaza
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Wani Farfesa a fannin kimiyyar siyasa na jami'ar jihar Nasarawa, Jideofor Adibe, ya bayyana ra'ayinsa kan babban zaben 2023 da aka kammala.
Farfesa Adibe ya bayyana cewa yanayin yadda aka gudanar da zaben 2023 kaɗai ya isa ya sa shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC), Mahmud Yakubu, ya yi murabus.
A cewar malamin jami'ar, idan aka yi la'akari da yadda masu sanya ido na cikin gida da na ƙasashen waje suka soki zaben 2023, ya kamata Farfesa Yakubu ya yi murabus.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana hakan ne a wata hira a cikin shirin karshen shekara na Channels TV mai taken, "2023: Year of Transition."
Meyasa ake ganin ya kamata Yakubu ya yi murabus?
A rahoton Vanguard, Farfesa Adibe ya ce:
"Ina tunanin na sha nanata wannan kalamai a lokuta da dama, tun a babban zaɓen 2019, INEC ba za ta taɓuka komai ba a yanzu saboda tana da rikici."
"Abu na farko da ya kamata a aiwatar shi ne Farfeda Mahmud ya tafi. Idan kana ganin ka yi bakin kokarinka amma masu sa ido na gida da na waje sun yi tir da zaben, ya kamata ka yi murabus."
"Na san rayuwarsa ba a nan ta dogara ba, don haka ka aje aiki saboda hukumar zaɓe ta ci gaba da riƙe darajarta ta mai gaskiya. Idan har ba a samu sauyi ba, babu wani sauran sa rai daga INEC."
Ya kuma caccaki Gwamnatin Tarayya bisa yaba wa INEC kan yadda aka gudanar da zaben, yana mai cewa “ba ta ba da damar sake yin garambawul a gudanar da zabe ba."
Shugaba Tinubu ya faɗi burinsa ɗaya tal a mulki
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya bayyana burinsa guda ɗaya tal wanda ya sa ya nemi kujerun mulki da dama har ya zama shugaban ƙasa
Shugaba Tinubu ya faɗi sirrin ne a jawabinsa na shigowar sabuwar shekara 2024 wanda ya yi ranar Litinin, 1 ga watan Janairu.
Asali: Legit.ng