2024: Shugaba Tinubu Ya Bayyana Babban Buri Ɗaya Tal da Ya Sa Ya Nemi Hawa Mulki Sau 3 a Najeriya
- Bola Ahmed Tinubu ya bayyana burinsa guda ɗaya tal wanda ya sa ya nemi kujerun mulki da dama har ya zama shugaban ƙasa
- Shugaba Tinubu ya faɗi sirrin ne a jawabinsa na shigowar sabuwar shekara 2024 wanda ya yi ranar Litinin, 1 ga watan Janairu
- A cewarsa, yana kokarin gina al'umma mai gakiya da adalci ta yadda kowane ɗan kasa zai samu dama daidai gwargwado
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja -Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana buri daya da ke sa shi ya tsaya takarar neman kujerar mulki a Najeriya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Idan zaku iya tunawa Bola Tinubu ya riƙe kujarar sanata a jamhuriya ta uku sannan kuma ya yi gwamna tsawon zango biyu a jihar Legas daga 1999 zuwa 2007.
A halin yanzu kuma shi ke riƙe da akalar mulkin Najeriya a matsayin shugaban masa bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene babban burin shugaba Tinubu?
Shugaban ya ce babban burinsa na tsayawa takara a wadannan ofisoshi shi ne "gina al'umma da adalci da kuma murƙushe rashin daidaito da rabuwar kan da ke kara ta'azzara."
Tinubu ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar na sabuwar shekara a ranar Litinin, 1 ga Janairu, 2024.
A cewarsa yana samar da yanayin da zai baiwa masu hannu da shuni damar cin gajiyar arzikin da suke samu, sannan kuma masu basira, hazikan ‘yan kasa su samu ci gaba a rayuwa.
Shugaba Tinubu ya ce:
"Babban burina a gwamnati a matsayina na Sanata a Jamhuriyya ta uku, gwamnan Legas na shekaru 8, da a yanzu Shugaban kasar nan mai albarka, shi ne gina al’umma mai gaskiya da adalci da kawar da rashin daidaito da ke kara ta’azzara."
“Yayin da na yi imanin ya kamata masu hannu da shuni su ci moriyar dukiyar da suka samu ta hanyar da ta dace, amma dole ne duk dan Najeriya da ya yi aiki tukuru da himma zai samu damar ci gaba a rayuwa."
"Tun da Allah bai halicce mu da basira da ƙarfi iri ɗaya ba, kowa zai samu alheri daidai gwargwadon yadda ya yi aiki tukuru, ba zai yuwu ya zama sakamako iri ɗaya ba."
Shugaban ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kowa zai samu dama daidai gwargwado don yin aiki tukuru da kuma samun ci gaba a wannan shekara, The Nation ta ruwaito.
Kakakin majalisar Ribas ya aje aiki gaba ɗaya
A wani rahoton kuma Shugaban majalisar dokokin jihar Ribas na tsagin Gwamna Fubara, Edision Ehie, ya yi murabus daga muƙaminsa, ya aje kujerar ɗan majalisa.
Honorabul Ehie ya aike da wasiƙa ga hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) amma bai ambaci dalilin yin murabus ɗin ba.
Asali: Legit.ng