Dole Gwamnatin Tarayya Ta Magance Matsin Tattalin Arziki a 2024, Atiku Ya Yi Batu Mai Daukar Hankali
- Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku ya mika sako ga gwamnatin Najeriya a yau Lahadi 31 ga watan Disamba
- Atiku ya nemi gwamnatin Najeriya ta zama mai tausayin talaka tare da kawo dokokin da za su taimaka a samu sauki a kasar
- ‘Yan Najeriya na ci gaba da kuka kan yadda tattalin arzikin kasar ke ci gaba da lalacewa da zama mai muni
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Najeriya - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya da ta magance matsalar tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fama dashi a 2024, rahoton TheCable.
Atiku ya yi wannan kiran ne a sakonsa na sabuwar shekara ta 2024 ga al’ummar kasar a karshen makon nan.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, Atiku ya nuna godiya ga Allah, inda godiya Allah bisa samun damar shiga sabuwar shekara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma siffanta 2023 a matsayin shekarar da ke cike da kalubale gareshi da ‘yan Najeriya, inda yace ya kamata kowa ya koyi darasi daga cikinta.
Abin da ya dami Atiku
A kalamansa, ya ce:
“Tashin farashin kayayyaki, dagulewar tattalin arzikinnmu da kuma lalacewar tsaron kasa da jihohinmu duk kalubale ne da ya kamata mu fuskanta a sabuwar shekara.”
Atiku ya soki dokokin gwamnati
Ya kuma soki gwamnatin kasar da sabbin dokokin da take kawowa, inda yace ‘yan kasuwa da jama’ar gari na gin illar hakan balo-balo.
Ya kuma yi kira ga a samar da tsari mai aiki din tabbatar da talakawan Najeriya sun samu ci gaban da ake bukata na dan Adam.
Hakazalika, ya nemi gwamnati ta tabbatar duk wasu dokokinta sun tafi daidai da kawo haske ga kasa ba wai shiri a cikin duhu ba, Punch ta tattaro.
Za a sayi littafin biliyan 3 ga ‘yan majalisa
Ana tsaka da kuka a Najeriya, an ware Naira biliyan 3 don siyan litattafai na dakin karatun majalisar dokokin Najeriya a kasafin kudin 2024.
Wannan yana kunshe ne a cikin lissafin kasafi na 2024 da majalisar ta amince dasji a jiya Asabar 30 ga watan Disamba, The Cable ta ruwaito.
Kamar yadda bayanin kasafin kudin ya nuna, an kuma ware Naira biliyan 12.12 don hidimar dakin karatu na majalisar dokoki ta kasa.
Asali: Legit.ng