Kano: Ciyamomin Kananan Hukumomi 44 Sun Maka Gwamna Abba a Kotu Kan Muhimman Abu 2

Kano: Ciyamomin Kananan Hukumomi 44 Sun Maka Gwamna Abba a Kotu Kan Muhimman Abu 2

  • Taƙaddama ta barke tsakanin kananan hukumomi 44 na jihar Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP
  • Ciyamomi 44 sun shigar da ƙara a gaban babbar kotun tarayya a Abuja suna neman a hana gwamnatin Kano amfani da kuɗinsu a ginin gadoji 2
  • Gwamna Abba ya sanya tubalin fara ginin gadojin sama guda biyu a birnin Kano ranar Jumu'a da yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shugabannin ƙananan hukumomi 44 sun maka gwamnatin jihar Kano a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja kan yunkurin gina gadoji biyu.

Ciyamomin sun kai ƙarar gwamnatin Abba Kabir Yusuf gaban kotun saboda yunkurin gina gadojin sama biyu a Tal'udu da Ɗan'agundi duk da kuɗin kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya damƙa ƙananan yara 7 hannun Iyayensu bayan ceto su, ya tura saƙo ga gwamnan Bauchi

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ciyamomin Kananan Hukumomi 44 Sun Maka Gwamnatin Kano a Kotu Kan Gina Gadoji 2 Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Sun buƙaci kotun ta bada umarnin hana gwamnatin Abba amfani da kuɗaɗensu na asusun haɗin guiwa wajen gina gadojin saman guda biyu a cikin kwaryar birni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ciyamomin sun shigar da wannan ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1733/2023 ranar Jumu'a, 29 ga watan Disamba, 2023.

Wadanda suka shigar da karar su ne kananan hukumomi 44 da kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON), reshen jihar Kano.

Sai kuma waɗanda ake ƙara sune gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Abba Kabir da kwamishinan shari'a kuma Antoni-Janar na jiha da Akanta janar na Kano.

Gwamna Abba ya kaddamar da fara aikin gadojin

Da yammacin jiya Jumu'a, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ɗora harsashin fara ginin manyan gadojin guda biyu.

A jawabinsa, Abba Gida-Gida ya ce bisa al'adar gwamnonin da suka gabace shi, za a samar da kuɗin waɗannan manyan ayyuka ne daga asusun haɗin guiwa na jiha da kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka bai wa ma'aikatan jihohinsu kyautar N100,000 a ƙarshen 2023

Ya kara da cewa idan aka kammala waɗannan gadoji, dukkan kananan hukumomin za su amfana da su lokaci bayan lokaci, rahoton Leadership.

Yusuf ya ce ya kirkiro wannan aikin ne da nufin sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa a cikin birni domin bunkasa harkokin zamantakewa da tattalin arziki a jihar.

Abba ya haɗa iyaye da yaransu bakwai

A wani rahoton kuma Gwamnan Abba Kabir Yusuf, ya damƙa kananan yara bakwai hannun iyayensu, waɗanda aka sato daga jihar Bauchi.

Abba ya gargaɗi iyayen su kara kulawa da taka tsan-tsan domin guje wa bara gurbi da ke ɗauke yara su sayar da su ga wasu mutane

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262