Kano: Babban Jigo Ya Faɗi Wanda Alamu Suka Nuna Zai Samu Nasara Tsakanin Abba da Gawuna a Kotun Koli
- Jigon jam'iyyar NNPP, Razaq Aderibigbe, ya bayyana kwarin guiwar cewa kotun koli zata yi adalici a shari'ar zaben gwamnan Kano
- Aderibigbe ya ƙara da cewa ya kamata a kara tunatar da waɗanda ke kan mulki cewa adalci shi ne mabuɗin nasara da ci gaba
- Da yake hira da Legit Hausa, jigon NNPP ya ce rashin adalci ke kawo tashe-tashen hankula wanda ke dakushe duk wani aikin ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Razaq Aderibigbe, babban jigon New Nigeria People's Party (NNPP) ya bayyana yaƙinin cewa kotun koli zata tabbatar da zabin al'ummar jihar Kano.
Mista Aderibigbe ya ce alamu sun nuna cewa alkalan kotun kolin Najeriya mutane ne masu gaskiya, waɗanda zasu yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da adalci da daidaito.
Jigon PDP ya jaddada yarda da kotun koli
Ɗan siyasan ya ƙara da cewa ya kamata masu riƙe da madafun iko su tuna cewa rashin adalci ke haddasa tashin yamutsi da karya doka da oda wanda ke hana ci gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon NNPP ya shaida wa Legit Hausa cewa:
"Duk da yunƙurin da ake na lullube gaskiya, jam'iyyar NNPP ta yi imanin cewa kotun koli zata tabbatar da muradi da zabin al'ummar Kano."
"Kotun koli za ta share duk wata tantama da ruɗani da suka baibaye hukuncin kotunan baya ba tare da tsoro ko fargaba ba."
"Mun yi imanin cewa hukuncin da kotun kolin Najeriya zata yanke zai ƙara tabbatar da zaman lafiya da tsaro da bin doka da oda a faɗin jihar Kano."
Kotun zabe ta tsige Abban Kano
Idan baku manta ba kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamna ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jama'iyyar NNPP.
Ta kuma bayyana ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna, a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.
Kotun ɗaukaka kara ta tabbatar da haka
Haka nan kuma Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta kori Abba daga matsayin gwamnan Kano.
Kotun ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe wacce ta tsige Abba ranar 20 ga watan Satumba, 2023.
Gwamnan PDP na shirin komawa APC
A wani rahoton na daban fitaccen malamin addini a jihar Legas, Primate Elijah Ayodele, ya ce Gwamna Siminalayi Fubara na Ribas zai tsallaka zuwa APC.
Legit Hausa ta tattaro Primate Ayodele na cewa wannan shiri na 'sauya sheƙa' wani ɓangare ne na babban kullin kawar da jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng