Jerin Gwamnonin da Suka Bai Wa Ma'aikata Jihohinsu Kyautar N100,000 a Karshen 2023
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Yayin da ƴan Najeriya ke shirye-shiryen bikin sabuwar shekara 2024, wasu gwamnoni sun ƙarƙare 2023 da ƙunshin kyauta mai gwabi ta N100,000 ga ma'aikatan jihohinsu.
Wannan kyautar kuɗi na zuwa ne yayin da mutane ke fama da matsin tattalin arziki wanda ya samo asali daga tuge tallafin man fetur da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi.
A nasa ɓangaren, shugaba Tinubu ya sha nanata cewa yana sane da halin ƙuncin da ƴan Najeriya suka shiga, yana mai tabbatar da cewa komai zai wuce.
Gabanin tafiya hutun kirsimeti, shugaban ƙasar ya sanar da ragin kaso 50 na kuɗin sufuri ga matafiyan jiha zuwa jiha yayin da masu hawa jirgin ƙasa kuma kyauta.
Kano: Gwamna Abba ya damƙa ƙananan yara 7 hannun Iyayensu bayan ceto su, ya tura saƙo ga gwamnan Bauchi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan haka ne wasu gwamnoni kusan uku suka sanar da bai wa ma’aikatan gwamnati a jahohinsu karin kudin kirsimeti masu kauri. A kasa ga cikakken bayanin gwamnonin.
1. Siminalayi Fubara
Duk da rigimar da ke tsakaninsa da uban gidansa na siyasa kuma tsohon gwamna, Nyesom Wike, Gwamna Fubara na Ribas ya sanar da baiwa ma'aikata kyautar N100,000 na kirsimeti.
Gwamnan ya bayar da kyautar naira dubu darin ne ga dukkan ma’aikatan gwamnati a ma’aikatu da hukumomi.
Wannan ne karo na farko da ma'aikatan jihar Ribas zasu koma gida da makudan kuɗi a matsayin kyautar bukukuwan kirsimeti, cewar rahoton Vanguard.
2. Francis Nwifuru
Bayan Fubara, gwamnan jihar Ebonyi ya amince da bai wa ma'aikata kyautar N100,000 a jiharsa da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, Channels tv ta tattaro.
A yayin wani taron ‘Renewed Hope Initiative Christmas Party’ a Abakaliki, gwamnan ya bayyana cewa:
“Bani ke gudanar da kananan hukumomi amma zan gana da ciyamo a yammacin yau. Dole ne kowane ma’aikaci ya samu Naira 100,000 daga wurinmu.”
3. Dapo Abiodun
Shi ma gwamnan jihar Ogun ba a barshi a baya ba, ya shiga cikin gwamnonin da suka amince da ware kuɗi masu tsoka na Kirsimeti ga ma’aikatan gwamnati.
A cewar jaridar The Guardian, alawus din ya fara ne daga kaso 68 zuwa kaso 159 na ainihin albashin ma’aikata, kuma ya shafi daga mataki na daya zuwa mataki na 17 na ma’aikatan jihar.
“A adadin kudi, mataki na 1-8 zasu samu kyautar N20,000, mataki na 9 da 10 (N25,000), mataki na 12 (N35,000), mataki na 13 da 14 (N40,000), mataki na 15 (N55,000), matakan 16 da 17 (N100,000)."
Gwamma Lawal Ya Kafa Tarihi a Jihar Zamfara
A wani rahoton na daban Dauda Lawal ya kafa tarihin zama gwamna na farko da ya fara biyan ma'aikatan gwamnati albashi wata 13 a shekara ɗaya a Zamfara.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a Gusau.
Asali: Legit.ng