Kujerun Yan Majalisa 26 Sun Fara Tangal-Tangal Yayin da PDP Ta Yanke Hukuncin Ƙarshe
- Jam'iyyar PDP ta ce ba gudu ba ja da baya kan kujerun ƴan majalisa 26 da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar Ribas
- Adeyemi Ajibade (SAN), bai bada shawara kan shari'a na PDP ya ce duk da Tinubu ya warware rikicin Ribas amma ƴan majalisar sun rasa kujerunsu
- Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ɗaga sauraron karar sauya sheƙar yan majalisar zuwa watan Janairu, 2024
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Peoples Democratic Party (PDP) ta jaddada matsayarta kan mambobin majalisar dokokin jihar Ribas 26 da suka sauya sheka zuwa APC.
Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ta ce har yanzu tana kan bakarta cewa ƴan majalisun da suka sauya sheƙar sun rasa kujerunsu a majalisar dokokin Ribas.
Mai bada shawara kan harkokin shari'a na PDP ta ƙasa, Adeyemi Ajibade (SAN), shi ne ya bayyana haka ga ƴan jarida a Abuja, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya faɗi wannan magana ne jim kaɗan bayan mai shari'a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ya ɗage sauraron ƙarar ƴan majalisar zuwa 24 ga watan Janairu, 2024.
Jam'iyyar PDP ta ɗauki matsaya ta karshe
Ajibade ya ce ko da yake shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya warware rikicin da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike, PDP ta tsayu kan abin da kundin tsarin mulki ya ce game da sauya sheka.
Channels tv ta rahoto a kalamansa ya ce:
"PDP a matsayinta na jam’iyya; muna tare da kundin tsarin mulkin kasar nan. Ba batun yarjejeniya ba ne, ana magana ne ta kwansutushin wanda duk mun rantse cewa za mu kiyaye."
"Gwamnan da kansa ya yi rantsuwar yin biyayya ga kundin tsarin mulki sau da ƙafa, haka nan shi ma Shugaban kasa. Ba ina adawa da sulhun shugaban ƙasa bane, yana da ikon tsoma baki a batun."
“Amma baya ga haka, mu a matsayinmu na jam’iyyar siyasa; PDP ce ta samu galaba a wadannan kujeru kuma tabbas muna sha'awar wadancan kujerun su dawo hannun mu."
Abba ya waiwayi masu buƙata ta musamman a Kano
A wani rahoton na daban Gwamna Abba Gida-Gida ya raba N20,000 ga mutane masu buƙata ta musamman (PWD) 2000 kowanen su a jihar Kano.
Da yake jawabi a wurin rabon tallafin, Gwamnan ya ce wannan somin taɓi ne domin ya san gudummawar da suka ba shi har ya ci zaɓe.
Asali: Legit.ng