Tsige Gwamna Abba: Hasashen Babban Malamin Addini Ya Bayyana Makomar NNPP da APC a Kotun Koli
- An buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano da ya yi addu’a kada a sake maimaita irin hukuncin kotun ɗaukaka ƙara a kotun ƙoli
- Fasto Kingsley Ndubuisi ya yi hasashen cewa Gwamna Yusuf zai sha kaye a hannun Nasir Yusuf Gawuna na APC a kotun ƙoli
- Kotun ɗaukaka ƙara dai ta tabbatar da hukuncin kotun zaɓe na tsige gwamnan saboda ba jam’iyyar NNPP ba ce ta ɗauki nauyin takararsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf wanda kotun ɗaukaka ƙara da kotun zaɓen gwamnan jihar Kano suka kora, ta iya yiwuwa ba zai yi sa’a ba a ƙarar da ya shigar gaban kotun ƙoli.
Hakan na zuwa ne yayin da Fasto Kingsley Okwuwe Ndubuisí, shugaban cocin Revival And Restoration Global Mission, ya yi hasashen makomar gwamnan na NNPP da takwaransa na APC, Nasiru Yusuf Gawuna a kotun ƙoli.
Kotun ƙoli za ta kori Gwamna Yusuf, Fasto Ndubuisi ya yi hasashe
Faston a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na YouTube a ranar Alhamis, 28 ga watan Disamba, ya ce Gwamna Yusuf na Kano zai fuskanci irin abin da ya haɗu da shi a kotunan baya a kotun ƙoli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ndubuisi ya ce Gwamna Yusuf zai sha kaye a kotun ƙoli, kuma jam’iyyar APC za ta mulki jihar ta hanyar yin kunnen uwar shegu da buƙatun jama’a.
Wani ɓangare na bayaninsa na cewa:
"Na ga gwamnan jihar Kano na yanzu yana barin ofishinsa, kuma wurin ya kasance cikin duhu, wannan alama ce ta cewa abin da ya faru a kotun ɗaukaka ƙara shi ne zai faru a kotun ƙoli."
Me ya sa kotun ɗaukaka ƙara, ta kori Gwamna Yusuf na Kano?
Idan ba a manta ba dai kotun zaɓe ta tsige Gwamna Yusuf ne a lokacin da aka cire ƙuri’u marasa inganci daga ƙuri’un da ya samu a zaɓen gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
Daga nan ne aka ayyana Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen. A ƙarar da ya shigar a kotun ɗaukaka ƙara, an tsige gwamnan saboda shi ba ɗan NNPP ba ne a lokacin da ya tsaya takara kuma ya ci zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar.
Sai dai Fasto Ndubuisi ya ce hasashen nasa na iya sauya wa idan gwamnan ya dage da addu'a.
An Fara Musayar Yawo Tsakanin gwamnatin Kano da APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa an fara musayar yawu tsakanin jam'iyyar APC da gwamnatin Kano kan batun wawushe N8bn daga asusun jihar.
A yayin da jam'iyyar APC ta yi zargin gwamnatin jihar na ƙoƙarin wawushe kuɗaɗen, gwamnatin ta musanta hakan inda ta bayyana hakan a matsayin yarfe na siyasa.
Asali: Legit.ng