Ganduje Ya Faɗi Matsala 1 Da Ke Neman Rusa Lissafin APC Gabanin Hukuncin Kotun Ƙolin Najeriya
- Dakta Abdullahi Ganduje ya nuna rashin jin daɗinsa bisa yadda rikici ya ɓarke a jam'iyyar APC reshen jihar Benuwai
- Shugaban APC na ƙasa ya buƙaci bangaren Gwamna Alia, shugabannin jam'iyya da ƴan majalisar na jihar su hakura su haɗa kansu
- A cewarsa, jam'iyyar mai mulki ta kinkimo babban aiki na dawo da martabar Najeriya amma matsalar na neman rusa mata lissafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya nuna damuwarsa kan rikicin cin gida da ya ɓarke a jam'iyyar reshen jihar Benuwai.
Ganduje, ya nuna rashin jin dadinsa game da rikicin da ya shiga tsakanin shugabannin APC na jihar, Gwamna Hyacinth Alia da kuma 'yan majalisar tarayya.
Bisa haka ne Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano ya yi kira ga ɓangarorin uku su maida wuƙarsu kube, su haɗa kawunsu a samu zaman lafiya, Leadership ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje ya yi wannan furucin ne yayin kaddamar da ginin sakateriyar APC da aka sabunta kuma aka raɗawa suna, 'Tinubu House' a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai ranar Laraba.
Muna bukatar zama tsintsiya ɗaya - Ganduje
Ya jaddada cewa hadin kai ne kadai hanyar da jam’iyyar za ta samu zaman lafiya kuma ta mai da hankali kan ci gaban jihar.
A rahoton Tribune, tsohon gwamnan ya ce:
"APC na aiki tukuru ƙarƙashin ajendar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, domin dawo da martabar Najeriya, kuma zamu cimma nasara ne kaɗai idan mun dunƙule wuri ɗaya."
"Muna alfahari da jam'iyyar APC ta Benue saboda wannan ginin da ta mana, jihar nan tamkar gida take a wurin APC. Mun ɗan tafi hutu ne amma yanzu mun dawo da karfi, mulki na hannun mu."
"Mun tsara yadda jam'iyya mai mulki zata cimma nasara shiyasa kuka ga kowane ofishin APC tun daga gunduma, kananan hukumomi jiha da na shiyya mun tsara yadda zasu tafiyar da ayyukansu."
Wannan kalamai na Ganduje na zuwa ne yayin da shari'ar zaben gwamnan Benuwai ta kai gaban kotun koli, wacce zata raba gardama tsakanin APC da PDP.
Hadimai sun fara aje aiki a Ondo
A wani rahoton kuma Rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu jiya Laraba ta kawo sabon sauyi a gwamnatin jihar Ondo kuma har an rantsar da sabon gwamna
Jim kaɗan bayan mutuwar Akeredolu, rahoto ya nuna akalla hadimai uku ne suka miƙa takardar murabus daga muƙamansu.
Asali: Legit.ng