Aiyedatiwa: Jerin Hadiman Gwamna da Suka Yi Murabus Daga Muƙamansu Bayan Mutuwa Ta Gitta
- Rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu jiya Laraba ta kawo sabon sauyi a gwamnatin jihar Ondo kuma har an rantsar da sabon gwamna
- Jim kaɗan bayan mutuwar Akeredolu, rahoto ya nuna akalla hadimai uku ne suka miƙa takardar murabus daga muƙamansu
- A cewarsu, sun ɗauki wannan matakin ne bayan rasa wanda ya ba su aiki yayin da Aiyedatiwa ya fara naɗa sabbin hadimai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Mutuwar tsohon gwamna, Rotimi Akeredolu, ya kawo sabon sauyi a gwamnatin jihar Ondo. Mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa ya karɓi rantsuwar kama aiki.
A rahoton Premium Times, akalla hadiman marigayi Akeredolu uku ne suka miƙa takardar murabus biyo bayan rantsar da Aiyedatiwa a matsayin cikakken gwamnan Ondo.
A ranar 13 ga watan Disamba, kakakin majalisar dokokin jihar Ondo ya ayyana Aiyedatiwa a matsayin muƙaddashin gwamnan jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma zama cikakken gwamma bayan mutuwar Akeredolu ranar Laraba, 27 ga watan da muke ciki.
Legit Hausa ta haɗo muku jerin sunayen hadiman tsohon gwamna da suka yi murabus, ga su kamar haka:
Adedoyin Adebowale
Babban mai taimakawa marigayi gwamna kan ayyuka na musamman da dabaru ya yi murabus daga muƙamin ranar Laraba a wata wasiƙa da ya miƙa wa sakataren gwamnatin Ondo.
A cewarsa, ya aje aikin nan take kuma ya nuna godiya ga gwammatin jihar bisa damar da ta ba shi na yi wa al'umma hidima.
Odebowale ɗan amutun marigayi tsohon gwamna ne kuma shi ne ya jagoranci yaƙi da mataimakin gwamna a lokacin rikicin siyasar da ya auku.
Richard Olatunde
Shi ne sakataren watsa labaran tsohon gwamna Akeredolu kuma ya miƙa takardar murabus daga muƙamin a ranar da tsohon gwamnan ya mutu.
Dama an yi tsammanin murabus din Olatunde yayin da sabon gwamnan ya naɗa Ebenezer Adeniyan a matsayin babban sakataren watsa labaransa.
Olatunde ya bayyana cewa murabus din nasa ya faru ne sakamakon mutuwar Akeredolu, wanda ya bayyana a matsayin uba.
Dare Aragbaiye
Mai ba Akeredolu shawara ta musamman kan harkokin ƙungiyoyi da wasu ayyuka ya miƙa takardar murabus ga sakataren gwamnati ranar Laraba.
Ya kuma bayyana rasuwar shugabansa a matsayin dalilin murabus din nasa, inda ya kara da cewa matakin zai fara aiki nan take.
Iyalan gwamnan da ya mutu sun magantu
A wani rahoton na daban Iyalan marigayi tsohon gwamna Oluwarotimi Akeredolu (SAN) sun nuna alhini yayin da suka tabbatar da rasuwar mai gidansu
A cewar iyalan, marigayi Akeredolu ya rasu ne a cikin bacci yayin da yake ƙarƙashin kulawar likitoci kan cutar da ke damunsa a Jamus
Asali: Legit.ng