Babban Dan Siyasa Ya Shiga Sahun Masu Neman Takarar Gwamna a Jihar PDP, Ya Fadi Muhimmin Dalili

Babban Dan Siyasa Ya Shiga Sahun Masu Neman Takarar Gwamna a Jihar PDP, Ya Fadi Muhimmin Dalili

  • Wanda aka kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da shi, Fasto Osagie Ize-Iyamu, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Edo a shekarar 2024
  • Fasto Ize-Iyamu ya bayyana cewa fahimtar da ya yi na siyasa da ayyukan gwamnati ya sanya shi ya fi dacewa ya jagoranci jihar
  • Faston na cocin RCCG wanda shine ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamna na 2020 ya bayyana hakan a ranar Laraba 27 ga watan Disamba a sakatariyar jam'iyyar ta jihar da ke Benin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Birnin Benin, jihar Edo - Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2020 a jihar Edo, Fasto Osagie Ize-Iyamu, ya bayyana aniyarsa ta shiga takarar gwamna a shekarar 2024 a jihar.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan jihar Ondo, Aiyedatiwa

Fasto Iyamu ya shiga takarar gwamnan Edo
Fasto Ize-Iyamu zai sake neman kujerar gwamnan Edo Hoto: @PastoIzeIyamu
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Ize-Iyamu ya bayyana aniyarsa a lokacin da ya gana da mambobin jam'iyyar APC na jihar a sakatariyar jam'iyyar a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba.

Fasto Ize-Iyamu yana son ceto jihar Edo

Wannan shi ne karo na uku da zai jarabawar sa'ar zama gwamnan jihar Edo, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Ize-Iyamu shekara mai zuwa tana da matuƙar muhimmanci a siyasar jihar.

A kalamansa:

"Muna buƙatar mu ceto jihar Edo daga mulkin rashin gaskiya daga hannun ƴan bani na iya. Sama da shekara bakwai mutanen Edo suna jure wa mulki ta hanyar farfaganda da ƙarya, da kuma amfani da cibiyoyin gwamnati domin cin zarafi da cin zalin jama’arta."

An shirya gudanar da zaɓen gwamnan jihar Edo a ranar 21 ga watan Satumban 2024. Jam’iyya mai mulki a jihar Edo ita ce jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Ondo ta fitar da sanarwa, ta faɗi abinda ya jawo mutuwar Gwamna Akeredolu

Tsohon Shugaban Daliban UNIBEN Ya Shiga Takarar Gwamna

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ɗaliban jami'ar Benin (UNIBEN), Michael Oshiobuhie ya fito takarar gwamnan jihar Edo ƙarƙashin jam'iyyar LP a zaben jihar na 2024 da ke matsowa.

Oshiobuhie ya bayyana cewa yana da tarin ilmi wanda zai sanya ya jagoranci jihar yadda ya kamata idan ya samu nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng