Awanni Kadan Bayan Shiga Ofis, Sabon Gwamna Lucky Ya Nada Mukamai, Ya Yi Wani Gagarumin Abu 1
- Sabon gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya nada sabbin mukamai awanni kadan bayan hawa karagar mulki
- Aiyedatiwa ya nada Ebenezer Adeniyan a matsayin sakataren yada labaransa da wasu mutane hudu mukamai daban-daban
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban ma'aikatan jihar, Omojuwa Olusegun ya fitar a yau Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Awanni kadan bayan hawa karagar mulki, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya nada sabon mukami.
Sabon gwamnan jihar Ondo ya nada Ebenezer Adeniyan a matsayin sakataren yada labaransa, cewar The Nation.
Yaushe sabon gwamnan ya yi nade-naden?
An bayyana hakan a cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban ma'aikata, Omojuwa Olusegun ya fitar a yau Laraba 27 ga watan Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olusegun ya ce sauran mukaman sun hada da Smart Omodunbi Jnr a matsayin hadiminsa a bangaren siyasa sai Abire Sunday Olugbenga hadimi a bangaren yada labarai na zamani.
Sauran sun hada da Motunrayo Oyedele hadima a bangaren daukar hoto sai Dakta Temitayo Iperepolu hadimi a bangaren aikace-aikacen, cewar Vanguard.
Wane mataki kuma sabon gwamnan ya dauka?
Gwamnan ya kuma ayyana kwanaki uku don hutu da kuma yin jimamin rasuwar tsohon gwamnan.
Ya kuma bukaci a saukar da tutuci kasa don nuna alhini kan rasuwar gwamnan a jihar da ya rasu a yau Laraba.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu a yau Laraba 27 ga watan Disamba a kasar Jamus.
Daga bisani, an rantsar da Lucky a matsayin sabon gwamnan jihar da yammacin yau Laraba a jihar da misalin karfe hudu na yamma.
Lucy Aiyedatiwa ya zama gwamnan Ondo
A wani labarin, A yau Laraba ce 27 ga watan Disamba aka rantsar da sabon gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa.
Lucky ya zama gwamnan ne bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu a yau Laraba bayan ya sha fama da jinya a kasar Jamus.
Wannan rahoto ya jero muku wasu muhimman abubuwa guda biyar game da sabon gwamnan da ya kama aiki a yau Laraba.
Asali: Legit.ng