Muhimman Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani Game da Sabon Gwamnan Jihar Ondo, Aiyedatiwa
Mukaddashin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya zama halastaccen gwamnan jihar.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
A rantsar da Aiyedatiwa ne bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu a yau Laraba 27 ga watan Disamba a Jamus.
Muhimman abubuwa game da sabon gwamnan
Lucky ya kama rantsuwar kama aiki ne a gaban Babban Alkalin jihar Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa 5 game da sabon gwamnan.
1. Ranar haihuwa
An haifi Aiyedatiwa a ranar 12 ga watan Janairun 1965 a Obe-Nla da ke karamar hukumar Ilaje da ke jihar, cewar The Nation.
2. Ilimi
Sabon gwamnan ya fara karatun firamare ne a Saint Peter's UNA a kauyen Obe Nla/Obe Adun da ke karamar hukumar Ilaje a jihar daga 1970 zuwa 1976
Har ila yau, gwamnan ya halarci makarantar sakandare a Ikosi da ke Ketu a Legas a 1982.
Ya samu takardar NCE a Legas a 1986 yayin da ya samu shaidar Diploma a Jami'ar Ibadan a 2001.
A shekarar 2013, ya samu shaidar kammala digiri na biyu kan harkokin kasuwanci a Jami'ar Liverpool da ke Ingila.
3. Siyasa
Lucky ya fara siyasa a shekarar 2011 inda ya kasance dan jam'iyyar ACN kafin maja da jam'iyyu inda ta dawo APC, cewar Daily Trust.
A shekarar 2015 ya nemi takarar dan Majalisar Tarayya a mazabar Ilaje/Ese-Odo kafin zama kwamishinan Tarayya daga 2018 zuwa 2019.
4. Mukamai
A shekarar 1982 zuwa 1983, Aiyedatiwa ya rike mai kula da sito a kamfanin Scoa Assembly Plant da ke Legas.
Ya samu mukamin mataimakin shugaban makarantar Reliance da ke Ibadan kafin ya rike mukamin manajan kasuwanci a kamfanin magani ta Universal da ke Legas a 1990.
Ya rike babban manajan kamfanin Blue Wall a shekarar 1996 kafin tsunduma harkar siyasa.
5. Mukami a gwamnatin Ondo
A ranar 25 ga watan Faburairun 2021 an rantsar da Rotimi Akeredolu a matsayin gwamna da kuma Aiyedatiwa mataimakin gwamnan jihar Ondo, cewar Tori News.
Ya zama mukaddashin gwamnan jihar daga watan Yuni zuwa Satumbar wannan shekara kafin daga bisani ya sake riƙe mukamin a ranar 12 ga watan Disamba.
An rantsar da Aiyedatiwa a matsayin gwamna
Kun ji cewa, Lucky Aiyedatiwa ya karbi rantsuwar kama mulki a matsayin gwamnan jihar Ondo.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar a yau Laraba 27 ga watan Disamba.
Asali: Legit.ng