Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Dan Takarar Gwamna a Jam'iyyar PDP Kan Dalili 1, Bayanai Sun Fito
- Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Ogun ya shiga hannun jami'an 'yan sanda kan zargin siyan kuri'u
- Wanda ake zargin, Hon. Ladi Adebutu ya na tsare ne a hannun 'yan sanda bayan zargin da Gwamnatin Tarayya ke yi a kansa
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Gwamna Dapo Abiodun ya fitar a shafin X a yau Laraba 27 ga watan Disamba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun - Rundunar 'yan sanda ta cafke dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Ogun, Hon. Ladi Adebutu.
Adebutu dai yanzu haka ya na tsare a hannun 'yan sanda kan zargin siyan kuri'u a zaben watan Maris da aka gudanar, Legit ta tattaro.
Mene ake zargin dan takarar gwamnan PDP?
Har ila yau, ana zargin dan takarar gwamnan da badakalar makudan kudade na biliyoyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Gwamna Dapo Abiodun ya fitar a shafin X a yau Laraba 27 ga watan Disamba.
Sanarwar ta ce ana tsare da Adebutu ne a ofishin Eleweran da ke jihar bayan halartar neman sa da aka yi tun farko kafin fita kasar waje.
Yaushe aka kama dan takarar gwamnan PDP?
An kama Adebutu bayan Gwamnatin Tarayya na zarginshi da laifuka da dama da suka shafi zabe da na badakalar kudade.
Har ila yau, dan takarar gwamnan jihar Ogun, Ladi Adebutu ya sha alwashin kwato kujerarshi a Kotun Koli.
Adebutu dai ya yi takara ne a jam'iyyar PDP a zaben da aka gudanar a watan Maris din wannan shekara.
An rantsar da sabon gwamnan jihar Ondo
A wani labarin, A yau Laraba 27 ga watan Disamba aka rantsar da sabon gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa.
Gwamnan ya karbi rantsuwar kama mulki ne bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu a yau Laraba a kasar Jamus.
Akeredolu ya rasu ne bayan fama da cutar daji da ya dade ya na fama da ita tun bayan zarcewa kan kujerar mulki.
Asali: Legit.ng