Mutuwar Akeredolu: An Saka Lokacin Rantsar da Lucky Aiyedatiwa Matsayin Gwamnan Ondo
- Rahotanni daga Akure, babban birnin jihar Ondo na nuni da cewa yau Laraba za a rantsar da Lucky Aiyedatiwa matsayin sabon gwamnan jihar
- Aiyedatiwa ya kasance mataimaki ga Gwamna Akeredolu (mai rasuwa) kuma mukaddashin gwamnan na tsawon makonni biyu
- Biyo bayan rasuwar Akeredolu, kundin mulkin Najeriya na 1999 kamar yadda aka sabunta ya ba Aiyedatiwa damar zama gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Ondo - A yau ne za a rantsar da mukaddashin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa a matsayin sabon gwamnan jihar.
Wannan lamari ya biyo bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu a yau Laraba, 27 ga watan Disamba 2023.
An saka lokacin rantsar da Lucky Aiyedatiwa
Wani rahoton Vanguard da ta tattaro a Akure, babban birnin jihar Ondo, cewa za a rantsar da Aiyedatiwa da karfe 4 na yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya mai tushe a majalisar dokokin jihar ta ce:
“Gaskiya ne za a rantsar da mukaddashin gwamnan a yau da karfe 4 na yamma."
"Yanzu baya jihar kuma da zarar ya dawo, babban alkalin jihar, Mai shari'a Olusegun Odusola, zai rantsar da shi a matsayin gwamna."
Idan ba a manta ba,kwamishiniyar yada labarai da wayar da kan jama'a ta jihar Mrs Bamidele Ademola-Olateju, ta sanar da rasuwar gwamnan a wata sanarwa a Akure.
The Nation a rahoton da ta fitar, ta ruwaito Ademola-Olateju, a cikin sanarwar, na bayyana Akeredolu, a matsayin shugaba na musamman.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Cikin jimami, gwamnatin jihar Ondo ta ke sanar da rasuwar gwamnan mu, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, SAN, CON."
Abin da tsarin kundin mulkin 1999 ya ce game da halin da jihar Ondo ke ciki
Da yake karin haske, wani lauya Barista Olatodun Hassan ya shaidawa Legit cewa, abu ne da ya zama dole kuma a bisa doka ya kamata a rantsar da Aiyedatiwa cikin gaggawa.
Ya ce:
“Wannan dabi’a ce ta siyasa idan babu gwamna, mataimakin gwamna ya na daukar matakin gaggawa.
“Mahimmancin hakan shi ne tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin mulki ba tare da wata matsala ba, kuma bai kamata a zauna ba gwamna ba, kuma doka ce".
A halin yanzu, sashe na 191 1 (1) na kundin tsarin mulkin 1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima, ya bayyana cewa:
“Mataimakin gwamnan jiha zai rike mukamin gwamnan jihar idan ofishin gwamna ya zama babu kowa saboda mutuwa, ko murabus, ko tsige shi, rashin iya aiki na dindindin.
"Ko kuma a tsige gwamna daga mukaminsa saboda wani dalili na daban bisa ga sashe na 188 ko 189 na wannan dokar."
Asali: Legit.ng